Fassarar jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa – da Musulmi a birnin Riyadh, Saudi Arabiya

.

11 ga watan Nuwamba, 2024

Bari in fara da miƙa godiyata ga Mai Martaba Sarki Salman Bin Abdul-Aziz Al-Saud, mai kula da Masallatan Harami guda biyu, da ya shirya wannan gagarumin taro.

  1. Tare da tsantsar girmama nauyin aiki da ya rataya akai na na tsaya a gabanku a yau yayin da muke ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin Falasɗinu da tabbatar da maslahar samar da ƙasashe biyu. Wannan manufar tana da matuƙar mahimmanci kuma al’amari ne na gaggawa.
  2. Rikicin Falasɗinu ya daɗe yana ci gaba da jawo wahalhalu marasa adadi ga mutane da dama. A matsayinmu na wakilan al’umma masu darajanta adalci, mutunci, da kuma ƙimar rayuwar ɗan Adam, muna da haƙƙi na mu kawo ƙarshen wannan rikicin.
  3. Ba zai wadatar ba in muka tsaya Allah wadai kaɗai. Dole ne duniya ta yi aiki don ganin an kawo ƙarshen ta’addancin da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda ya ƙi ci yaƙi cinyewa. Babu wata manufa ta siyasa, ko dabarun soji, ko kuma rashin tsaro da ya kamata ya bada damar salwantar da rayukan da ba su ji ba basu gani ba.
  4. A cikin tushen ƙa’idodi na tsarin ƙasa da ƙasa, ƙasashe suna da ‘yancin kare kansu. Amma a yayin kare kai dole ne a yi la’akari da daidaito da yin sa daidai da tsarin doka, diflomasiya da tsarin gudanarwa na duniya. Ba zai yiwu a hallaka gaba ɗayan farar hula ba, da burinsu da makomarsu a ƙoƙarin yin hakan ba.
  5. Taimakon jin ƙai ba gata ba ne, haƙƙin ɗan Adam ne. Babu wani mutum ko ɗan ƙasa ne, ko wata ƙabila, ko wani addini, da za a hana shi samun tallafin a lokutan rikici. Dole ne kuma mu tabbatar da cewa ma’aikatan jin ƙai dake gaba-gaba suna cikin aminci da ƙoshin lafiya don gudanar da aikinsu a Gaza.

Manyan baƙi masu daraja,

  1. Samar da zaman lafiya a tsakanin ƙasashen biyu, ya kasance wani ginshikin ne na sabunta fata, wanda ke wakiltar haƙƙoƙin Isra’ila da Falasɗinawa na tabbatar da ‘yancin kai da zaman lafiya. Ba batun diflomasiyya kawai bane; hangen nesa ne da ake son tabbatar da shi bisa ƙa’idojin daidaito da fahimtar juna.
  2. Cimma wannan hangen nesa yana buƙatar sadaukar da kai don tattaunawa da mutunta tarihi. Dukanmu mun san cewa wannan rikici bai fara ba a ranar 7 ga Oktoba 2023. Za a iya warware shi ta hanyar sasantawa bisa ƙa’ida, da kyakyawar fahimta.
  3. Wannan rigima, tun farkon tarihi abu ne da ke da ban mamaki ta inda rarrabuwar kan ya bazu cikin sauri. Tasirin hakan ya haifar da tashin hankali mara iyaka, inda zaka samu ya yafu har a wayoyin hannu sama biliyan a duniya. Muna buƙatar nemo sabbin hanyoyin samar da zaman lafiya cikin gaggawa.
  4. A koda yaushe Najeriya na jajircewa wajen samar da zaman lafiya da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe. Abubuwan da suka faru a cikin ƙasar mu sun koya mana cewa siyasa ba ta zama madadin mutunta bambance-bambancen mu ba.
  5. Hanyar sulhu na iya kasancewa cike da ƙalubale, amma ta hanyar tattaunawa ta gaskiya ne za mu iya samar da fahimta. Ƙasashen duniya na da damar kawo sabbin tunani kan wannan ƙalubalen. Ya zama wajibi mu yi wannan tattaunawa cikin ikhlasi, tare da sanin irin sarƙaƙiyar da kowane ɓangare ke fuskanta.

Ranka ya daɗe Sarki,

  1. Kada mu manta da halin da ƴan Adam ke shiga sanadiyyar wannan rikici. Dole ne mu ba da fifiko ga muryoyin iyalan da aka ɗaiɗaita, yaran da suka girma cikin tsoro, da kuma al’ummomin da ke son samun kwanciyar hankali. Haƙƙin ne da ya rataya a wuyanmu mu kwato musu haƙƙin su da gina musu makoma inda mafarkinsu ba zai rushe ba.
  2. Ina kira ga dukkanmu da mu taru a kan haɗin kai, mu tsaya tsayin daka kan ƙudurin mu, mu yi ƙoƙarin ganin mun zauna lafiya, ba tare da tsoro da tashin hankali ba. Tare, za mu iya tabbatar da ƙudurin samar da ƙasashe biyu, wanda ke ƙunshe da alƙawarin samar da gobe mai inganci ga kowa.
  3. A ƙarshe, Najeriya na kira da a samar da wata sakatariya da ta ƙunshi zaɓaɓɓun shugabannin gwamnatoci (ko manyan wakilansu) don yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen duniya, ba da tallafi, da sa ido kan aiwatar da ƙudurin taron, da bayar da rahotanni akai-akai ga shugabannin haɗin gwiwar OIC da Larabawa har sai an samu zaman lafiya na dindindin.
  4. Na gode muku duka.