Fassarar Sakon Zauren Dattawan Arewa (NEF) Akan Matsalar Tsaro a Arewa

Wannan zaure na dattawan arewa, kamar sauran yan kasa, ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa manoma a gonakinsu, dake kauyen Zabarmari a jihar Borno, da kuma yawan kashe-kashen da ke faruwa kullum a wannan yanki na Arewa. Mun jima mu na daga muryarmu akan matsalar tsaro a wannan yanki. Ba kuma mu taba yin kasa a guiwa ba, wurin kira ga gwamnati da ta sauya salo akan irin halin ko in kula da take nunawa matsalar. Musamman matsalar Boko Haram, satar shanu, hare hare akan mutanen kauyuka da sauransu. Mun kuma sha janwo hankalin gwamnati akan yadda za ta inganta harkar tsaro, ta kuma kawo gyara a yanayin jagorancin shugabannin tsaron, amma duk wannan bai sa shugaba Buhari ya canja ba, hasali ma, kunnen uwar shegu yayi da shawarwarin da muke ba shi.

Kamar yadda aka saba, a wannan karon ma, gwamnatin bata bamu kunya ba, in aka yi la’akari da jawaban da mai baiwa shugaban qasa shawara na musamman yayi akan matsalar, ya nuna halin rashin damuwa da halin da mutane suke ciki. Domin kuwa ya kawo wata karkatacciyar hujjarsa ta cewa “Manoman basu nemi izini a gurin jami’an tsaro ba, kafin su shiga gonakinsu”. Wanda hakan ke nuna, shifcin gizo ne kawai, da ake gaya wa duniya, sojojin Nijeriya, sun fatattaki yan ta’adda daga yankunan.

Wadannan kashe kashe da ake yi a kullum, na nuna cewa, da wuya mutane su amince da su koma garuruwan su, su kuma cigaba da sana’o’insu, domin samun habakar tattalin arziki da komowar zaman lafiya mai dorewa, ko da kuwa ga gwamnatin da ta dau abin da muhimmanci. Wanda a iya fahimtar mu, wannan ba shi ne abinda ya damu wannan gwamnati ba.

A bangarori da yawa na yankin arewa, manoma sun kasa zuwa gonakinsu domin suyi noma. Saboda tsoron abinda ka je ya dawo. yan wadanda suka yi karfin hali suka yi shuka, su kansu sun kasa zuwa su girbe abinda suka shuka saboda tsoro. Hakan na nuni da cewa, in ba mataki aka dauka ba, to bana yunwa zata gallabi al’ummar kasar nan. Saboda rashin tsaro da ya hana su noma a wannan shekara.

A qarkashin kulawar wannan gwamnati, mun lura da cewa, rayukan mutane sun zama ba a bakin komai ba. Rashin daukan tsauraran matakai ya sanya, a yau fashi, sata, kisan kai ya zama abin kafullo a wurin mutane. Kuma babu wata shaida daga shugaba Buhari na cewa, yana da niyyar tashi tsaye domin kare rantsuwar da yayi a yayin kama mulkinsa, cewa zai kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A qasashen da aka san mutuncin dan adam, in har shugaba ya gaza samar da tsaro ga al’ummar da ya ke mulka, to aje mukaminsa yake.

Hakeem Baba Ahmad
Darektan Hulda da jamaa da wayar da kai na Zauren Dattawan Arewa

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*