
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kula da Birnin Tarayya Abuja, FCTA ta aika saƙon gargaɗi ga masu karɓar haraji daga mutane da cin zarafinsu musamman masu motoci a birnin.
Kwamishinan ƴan sandan Abuja, Olatunji Disu ya bayyana hakan bayan taron Majalisar Tsaro a ranar Juma’a a inda ya yi kira ga mazauna da matuƙa motoci da su aika wa ƴan sanda rahoton duk wani da ya ci zarafinsu da sunan karɓar haraji.
Ana yi wa masu irin aikin laƙabi da ‘AMAC boys’ waɗanda suka bazu a duka ƙananan hukumomi shida na birnin, saidai ayyukansu sun fi yawa a yankunan Kubwa da ƙaramar hukumar Buwari da kuma ƙwaryar birni, wato ƙaramar hukumar AMAC.
Kwamishinan ya bayyana wa manema labarai cewa mafi yawancin ayyukan AMAC boys sun fi shafar waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, ya na mai cewa sun ɗauki matakan dakatar da hakan acikin al’umma.
Ya ƙara da cewa za su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran hukumomin tsaro don ganin an daƙile ayyukan waɗannan ɓata-gari a ƙoƙarinsu na ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar al’umma.