Hukumar ƙwallon ƙafar Duniya (FIFA), ta fitar da jadawalin Gasar Kofin Duniya da za a doka.
An sanya ƙungiyar Palmeiras ta ƙasar Brazil da takwararta ta ƙasar Portugal Porto a rukunin “A” tare da ƙungiyar Inter Miami ta jagoran kofin duniya dan ƙasar Argentina Messi wanda FIFA ta bata gurbi bayan da ta yi zarra a gasar MLS ta wannan kakar.
Lionel Messi da ƙungiyar Inter Miami za su ƙaddamar da gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi 32 da Hukumar ƙwallon ƙafar Duniya (FIFA) ta ƙirƙira, lokacin da babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafar za ta haɗu da takwararta ta ƙasar masar Al-Ahly yayin buɗe gasar a ranar 15 ga watan Yuni mai zuwa.
An sanya ƙungiyar Palmeiras ta ƙasar Brazil da takwararta ta ƙasar Portugal Porto a rukunin “A” tare da ƙungiyar Inter Miami ta jagoran kofin duniya ɗan ƙasar Argentina Messi wanda FIFA ta bata gurbi bayan da ta yi zarra a gasar MLS ta wannan kakar.
Dan tsohuwar ƙungiyar Messi ta Barcelona, ɗan asalin Brazil, Neymar, zai sake haduwa da abokan dabinsa na gasar La Liga kuma zakarun nahiyar Turai Real Madrid a rukunin “H”.
Kungiyoyin nahiyar Turai 12 ne za su fafata a gasar inda Manchester City za ta haɗu da Juɓentus a rukunin “G”.
An sanya kulub ɗin PSG a rukuni mai zafi tare da Atletico Madrid da kungiyar Botafogo da ta lashe gasar Copa Libertadores ta kasar Brazil da kuma Seatle Sounders.
Jami’an ƙungiyoyi da tsofaffin ‘yan wasa sun taru domin fitar da jadawalin na ranar Alhamis a birnin Miami sannan zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya aike da sakon fatan alheri ta bidiyo gabanin fara bikin, wanda ya gudana yayin wani shirin talabijin na mintuna 90 da aka yaɗa kai tsaye daga ɗakin gabatar da shirye-shiryen tashar da ke Miami.
Za a buga wasan ƙarshe na gasar a filin wasa na Metlife da ke New Jersey a ranar 13 ga watan Yuli mai zuwa.