FIFA za ta biya kuɗin fafatawa a kofin duniya ga asusun ’yan wasa kai tsaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Duniya (FIFA) ta sanar da aniyarta ta biyan kuɗaɗen da ake bai wa duk tawagar da aka dama da ita a gasar kofin duniya ta Australia da New Zeland kai tsaye ga asusun ajiyar ’yan wasan maimakon ta biya hukumar ƙwallon ƙafar ƙasashensu.

Ta shafi tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya, Super Falcons.

Tun da farko an jiyo kocin tawagar Falcons ɗin, Randy Waldrum yana cewa akwai wasu ’yan wasan tawagar da har yanzu suke bin haƙƙoƙinsu tsawon shekaru biyu.

Wannan lamari dai ya janyo tada jijiyoyin wuya, inda har ya kusan yin mummunan tasiri a kan shirye-shiryen da Falcons ɗin ke yi, bayan da ’yan wasan suka yi barazanar janyewa daga atisaye.

A cikin bidiyo, Samoura ta ce FIFA za ta sa ido a kan abin da ya shafi biyan alawus-alawus na ’yan wasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *