Filato: An tsige DPO bisa zargin kashe wasu makiyaya biyu

Daga BASHIR ISAH

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Filato, Edward Egbuka, ya tsige tare da tsare DPO mai kula da yankin ƙaramar hukumar Bassa a jihar, wato DSP Solomon Machu, bisa zargin kisan wasu makiyaya biyu a jihar.

An zargi DPOn ne da kashe Musa Giwa ɗan shekara 24, da Ibrahim Sa’idu ɗan shekara 30, ta hanyar mafani da bindiga
bayan da ‘yan bijilanti na yankin suka kama makiyayan a ƙauyen Dogon Daji tare da miƙa su ga DPOn cikin ƙoshin lafiya a Lahadin da ta gabata.

Manhaja ta tattaro cewa a Alhamis da ta gabata ‘yan sanda suka miƙa gawarwakin Musa da Ibrahim ga ‘yan’uwansu domin yi musu jana’iza.

Harɗon Dogon Daji, Alhaji Adamu Muhammad, ya ce ɗaya daga cikin marigayan Bafulatani ne yayin da gudan Ganawuri. Ya ce su biyun sun tafi neman wata sanuwar ɗan’uwansu ne da ta ɓata inda suka gamu da ‘yan bijilanti suka kama su tare da miƙa su ga DPO Machu.

Harɗon ya ce abokan tafiyansu sun dawo gida bayan da aka ga sanuwar da aka je nema in banda Musa da Ibarhim. Ganin haka ya ce sai ya kira Sarkin ƙauyen Dogon Daji, Mr. Musa Garba Asibayi, inda ya sanar da shi a kan ya taimaka ya duba ko matasan na yankinsa.

Amma daga bisani, sai Sarkin ya kira shi a waya tare da sanar da shi cewa ‘yan bijilanti sun kama su sun miƙa su ga DPO.

Alhaji Muhammad ya ce a safiyar Litinin da ta gabata aka gano gawarwakin marigayan a bakin hanya kowannensu ɗauke da alamar harbin bindiga a kansa.

Iyayen Musa da Ibrahim sun ce suna buƙatar a bi musu haƙƙin ‘ya’yansu da aka kashe.