Filisɗine ta aika wa gwamnatin najeriya wata takarda a ranar 27 ga watan Yuni, inda ta buƙaci Najeriya ta aminta da Filisɗine a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Bayan nan, sun yi kira ga ƙasashe da su taimaka wajen ganin an gurfanar da Isra’ila gaban kotun duniya sabida laifuka yaƙi da suka tabka a harin da suke kaiwa Filisɗine din wanda ya shafe watanni ana fama dashi.
A cewar takardar, kullum alƙaluman da ke fitowa daga Filisɗine abun tsoro ne. Kuma sun koka da yadda cewa duk wani dokar ƙasa da ƙasa baya aiki in dai ƙasashen yamma sun nuna basa so. Ƙasar Isra’ila ta samu tallafi aƙalla dala biliyan 6.5 a fannin tsaro daga ƙasar Amurka a wani rahoton gidan jaridar Washington Post.
Ya zuwa 24 ga watan Yuni, Filisɗinawa 37,718 ne suka rasa rayukansu da wasu 86,377 suka ji raunuka, wanda mafi akasarin su mata ne da yara. A zirin Gaza, yara sun daina zuwa makaranta aƙalla wata takwas kenan saboda tsoron me zai je ya dawo.Kwamishina janar na majalisar ɗinkin duniya, Larzarrani philippe ya shaida cewa a kowanne rana, aƙalla yara goma na rasa ƙafafuwansu.
Tunda fara wannan yaƙi, Ƙasar Isra’ila ta ki faɗan adadin waɗanda ke tsare a wajensu. Banda cin zarafin ɗan Adam da kullum suke fuskanta irin wanda dokar ƙasa da ƙasa tai Allah wadai dashi. Saboda hakane, Filisɗine ke bukatar ƙasar Najeriya da sauran ƙasashen duniya da su taimaka wajen ganin an gurfanar da Isra’ila domin ta amsa laifukan yaƙi da kisan gilla da take yi.
Sannan sun buƙaci Najeriya ta aminta da Filisɗine a mastayin ƙasa mai cin gashin kanta kamar yadda takwarar ta ƙasar Armenia ta tabbatar a satin da ta gabata.