Fim ɗin wata karuwa ‘Anora’ ya lashe Oscars tare da kyaututtuka biyar 

Daraktan ‘Anora’  ya lashe Oscar a matsayin mafificin darakta 

Daga AISHA ASAS 

Mai shirya finafinai Sean Baker ya lashes kyautar Academy a matsayin  mafificin darakta da fim ɗinsa mai suna ‘Anora’. Wannan fim ɗin an gina shi kan rayuwar wata karuwa ce mai rawar nishaɗi da jan hankali da rayuwarta ta rikiɗe a lokacin da ta auri ɗan babban hamshaƙin ɗan kasuwan Rasha.

Baker ya samu sa’ar lashe kyautar darakta, bayan ya karɓi lambobin girma daga ƙungiyoyi kamar ƙungiyar haɗakar daraktoci ta Amurka( Directors Guild of America), da ƙungiyar haɗakar masu shirya finafinai ta Amurka( Producers Guild of America). Ya kuma samu kyautar darakta daga Film Independent Spirit Award’.

Aikin farkon da ya fara fitar da wannan mai shirya finafinai shi ne, ‘Tangerine’. Wanda ya kasance fim ɗin barkwanci da aka yi  akan rayuwar karuwar da ta canza jinsi a garin Los Angeles, wanda shi wannan fim ɗin an ɗauke shi ne a wayar iPhone. Sai fim ɗinshi na gaba ‘The Florida Project’ wanda ya alƙiblanci ƙalubalen da iyalan da ke zaune kusa da walt Disney world(wurin wasan cartoon) ke fuskanta. Inda ya haska labari akan wata bazawara mai ‘ya’ya da wani manaja na gidajen kwanan na kan hanya wato, ‘roadside motel’ da suka ɗau haramar kare mutuncin yarinya ‘yar shekara shida.

fim ɗin Baker na gaba, ‘Red Rocket’ wanda ya haska rayuwar ɗan wasan finafinan basta da aka dena yayi a Teɗas. Sai sabon fim ɗinshi ‘Arora’ wanda wani mai sharhi ya yi wa laƙaɓi da “bawdy modern fable” ( labarin batsa na zamani da ke ɗauke da lurarwa. 

Fim ɗin ya samu shiga layin tantancewa har shida (nomination), ciki har da na fim mafi kyan hotuna.

Daga cikin waɗanda suka shiga layin tantancewar a ɓangaren  daraktoci akwai; Brady Corbet da fim ɗin ‘The Brutaliat’, James Mangold da fim ɗin ‘A Complete Unknown’, Jacƙues Audiard da fim ɗin ‘Emilia Perez’, da kuma Corale Fargeat da ‘The Substance’.