Fim saƙo ne, kada a yawaita tunanin kuɗi da ɗaukaka yayin yinsa – Naziru Alkanawy

“Komawar kasuwancin fim yanar gizo dama ce da ba a taɓa samun irinta ba”

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano 

Naziru Alkanawy yana ɗaya daga cikin marubutan labarin finafinai da suka yi suna a cikin masana’antar Kannywwod, domin kuwa ya daɗe a harkar kuma duk wani babban labarin fim da ya fita ya yi suna a duniya za ka ga yana da sa hannu a ciki, musamman a tashar Arewa 24 da kuma labarun dirama na BBC da suke gabatarwa. A yanzu Naziru Alkanawy yana a matsayin mai zaman kansa kuma shine yake da shafin Rariya na YouTube da suke ɗora manyan finafinan Hausa. Domin jin ko wane ne Marubuci Naziru Alkanawy, Wakilin Blueprint Manhaja, Mukhtar Yakubu, ya samu tattaunawa da shi. Don haka sai ku biyo mu, domin ku ji yadda ta kasance:

MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kan ka ga masu karatunmu.
ALKANAWY: To ni dai suna Naziru Alkanawy kamar yadda sunana ya nuna. Ni mutumin Kano ne, a Kano aka haife ni, a nan na taso, kuma kamar yadda mutane suka sani marubuci ne da na fi raja’a a rubutun finafinan Hausa.

To da yake ka ɗauki dogon lokaci kana yin rubutu kamar yadda tarihinka ya nuna. Ko ya ya tasirin rubutun yake a gare ka?
Gaskiya kusan komai na rayuwa rubutu ya yi tasiri a gare shi, don babu wani abu na rayuwa ta wanda rubutu bai yi tasiri a cikin sa ba. Domin akwai wasu lokutan da nake so na zauna na yi wani abu wanda rubutun bai shiga cikin sa ba, amma sai ka ga rubutun ya shiga musamman rubutun fim, don nakan soma rubutun littafi, amma daga baya sai ya koma na fim.

A cikin rubutun da ka yi na fim masu karatu za su jin wasu ko da ba duka ba.
To wannan wani abu ne da sai na tsaya na yi nazari, domin suna da yawa, amma dai akwai ‘Ɓarauniya’ Kashi na 2. Akwai ‘Sulɗana’, ‘Larai ko Jimmai’, suna da yawa dai, sai kuma waɗanda na yi wa cibiyoyi da wasu kamfanini kamar akwai aikin da na yi da wata hukuma ta masu kula da yara marasa galihu a Africa wani fim da muka yi ‘Fitsarin faƙo’, akwai wata hukumar da na yi mata aikin rubutun fim na yadda za a kawo ƙarshen cin hanci da rashawa da sauran cibiyoyi da ƙungiyoyi da muka yi aiki da su, ko in ce muna kan yi har yanzu.

Ka na matsayin marubucin fim ko ya aka yi ka rikiɗe ka zama furodusa?
To a zarihi mutane za su ce na rikiɗe na zama furodusa, amma tun da na shigo harkar Ina kallon kaina a matsayin furodusa ne, don na shigo ne don na bada gudunmawa ga mutane, to amma akwai wata doka ta rayuwa, duk abin da za ka shiga, to lallai kana buƙatar ilimi a cikin sa, don haka dole ka nemi ilimi domin ka san rawar da za ka taka a cikin sa, don haka mafarki na ne da na shigo da shi a yanzu yake tabbata, domin burina shi ne na tara jama’a ya zama Ina koyar da su suna cin abinci a ƙarƙashina, to shi ne manufar da nake da ita ta shigowa harkar fim.

A daidai lokacin da ka samu kan ka a cikin harkar sai kuma kasuwar ta tashi da Ƙofar Wambai ta koma online. Ko ya ka samu kan ka a daidai wannan lokacin?
Ko da kasuwancin ya koma online, farkon abin da na fara kallo a matsayin tarnaƙi a gare ni, idan zan shiga domin ko a baya da a ke gudanar da kasuwancin Ƙofar Wambai lallai na ga kasuwar ba ta yi daidai da yadda nake so na tsara tawa ba, don haka har sai da aka zo daidai wannan lokacin da a ke yi duk da dai a farko mutane sun ɗara hannu a ka suna ta wayyo Allah an rasa makama, to ni kuma a lokacin ne na yi tunanin tsara yadda zan tafiyar da tsarin na wa, kuma sai na hango wata babbar kasuwar da ba a tava samun wadda ta kai ta ba, kuma duk wani da yake yin harkar fasaha to a yanzu ne ya kamata ya fito da hajar sa ya baza, domin ya ci moriyar abin da ya daɗe yana wahaltawa, to gaskiya na kalli kasuwancin fim da ya koma online wata dama ce da ba a tava samun wadda ta kai ta ba.

Ka san su abin da suke kallo shi ne, kasuwancin ‘online’ ba kasuwar da za ka saka kayan ka a gaba kana kallon sa ba, kawai dai za ka zuba shi ne ba ka san inda yake ba, don haka mutane har yanzu ba su gama sakin jiki da shi ba wasu kuma da suka shiga sai suka rinƙa yin asara don haka suka ja baya.

To ai ka ga dukkanmu mun sani cewar da wanda ya sani da wanda bai sani ba, to ba za su taɓa zama ɗaya ba, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa a baya na ɗauki tsawon lokaci ba yi wani abu ko ɗaya ba, saboda Ina ta neman sani da kuma bibiyar hanyoyin da suka dace, domin kowanne mutum akwai aikin da ya dace da shi, domin akwai wanda in ana buqatar aikin ƙarfi, to da gudu zai halarci wajen, don haka duk wanda zai shiga kasuwancin fim na online, to lallai yana buƙatar ya san ya ya kasuwancin yake, ya kuma san daɗi da rashin daɗin sa da kuma ƙalubalen da yake cikin sa saboda ya shirya idan zai shigo, idan har ba zai iya daurewa ba, to gaskiya ba zai kai ga nasarar da yake so ya kai ba. Amma fa sau da yawa idan mutane suka shiga harkar, sai ka ga mutane kaɗan ne suke iya daurewa.

Bari na ba ka misali, akwai wata babbar Plaza da aka gina a Kano kowa ya san ta, shekarar farko da mutanen da suka kama hanya a wajen sai kowa ya kasa biyan kuɗin haya, sai Lauya ya sanar da mai gidan ba a biya kuɗin haya ba, to sai aka saka ranar da idan mutum bai kawo kuɗin ba za a rufe shagon sa, to lallai an rufe shagunan mutane da yawa wasu kuma daqar sun je sun samo kuɗin sun biya. To da aka biya sai maigidan ya tara mutanen da kuma lauyansa, ya sanar da su cewar kowa a mayar masa da kuɗin sa da ya biya, suka ji daɗi sosai.

Sai ya ce, abin da ya sa ya matsa a kan lallai sai kowa ya biya kuma har aka rufe na wasu shine, don ya nuna wa mutane cewar wannan waje wajibi ne sai kowa ya biya kuɗin haya, don haka kullum ka rinƙa tunanin yadda za ka biya wannan kuɗin saboda matsala irin wannan ko za ta iya faruwa, don haka shi kasuwanci idan za ka fara shi, ya kamata a ce aƙalla ka yi kasafi na shekara 3 ka ware dukkan abin da kasuwancin ka zai buƙata daga gare ka, wannan yana nufin za ka ware kuɗin haya da shekara 3 kenan, don haka kuskure ne babba mutum ya fara kasuwanci a shekara ya ce, yana so ya ga ribar wannan kasuwancin, don haka magana ta gaskiya kasuwanci yana farawa ne da raino, domin idan mun kula za mu ga mu kan mu ai ba haka aka haife mu ba, jarirai aka haife mu har muka fara tafiya muka kawo yadda muke a yanzu, don haka shi tsari na Ubangiji komai yana tafiya ne mataki mataki.

Don haka babu yadda za a yi ka fara harka lokaci guda ka ce kana so sai ka zama wani, akwai hidimar akwai bauta da sauran abubuwa da za a yi. Ita ribar tana zuwa ne bayan duk ka yi waɗannan abubuwan, domin duk waɗanda suke cin gajiyar abin a yanzu, idan aka koma baya za a ga irin wahalar da suka sha wanda mu ba mu sani ba, kawai nasarar su muka gani a yanzu. amma idan aka bi daddijin abin za a ga ai har yanzu ma ba a fanshi wahalar da aka yi ba amma dai ana kallon su cikin jin daɗi.

To a yanzu za a iya cewa ka cimma nasara kenan?
Ai ka san kowacce nasara tana da ma’anar ta a wajen mutune daban daban, don haka idan zan kalli nasara a kaina zan iya cewa Ina ganin nasarori da yawa, domin kamar yadda na faɗa maka tun da na shigo masana’antar nan ya zama aiki nake bayarwa don wasu mutane su samu aiki a tare da ni kowa ya yi aiki na biya shi don ya ji daɗi a ran sa, don haka idan na kalli abin ta wannan sigar sai na ga na yi nasara mai girma, don yanzu akwai ma’aikata na da kuma jaruman da suke yi mini aiki wanda a baya idan Ina yin aikin ana yi mini dariya saboda su ba wasu ba ne waye zai kalli waɗannan. An faɗa mini haka sau da yawa, amma dai na ci gaba da aikin da su, kuma sai Allah ya sa aka karɗe su, don a yanzu in dai za a yi wani babban fim yana da wahala a ce babu ɗaya daga cikinsu, kuma ana kallon su a matsayin jaruman da suke tashe a yanzu to shi ne nasara ta da nake ganin na yi.

A yanzu wanne buri ka sa a gaba?
Burin dai da na saka a gaba shi ne, wannan tashar da na ke ginawa, don ni na ɗauki shekaru ne masu yawa kuma har yanzu ban kai ga ɗaya cikin 10 ba wanda na ke so zuwa lokacin da na ɗauka na ga za ta cika mini wannan burin, don gaskiya wannan finafinan da na fara wata tafiya ce mai tsayi da na ɗakko amma wajen da na ke so na je a tafiyar yana da nisa burin kuma ba wani ba ne shi ne na ga na samar da wata tasha mai girma a duniya kamar Nexfilx yadda mutane za su rinƙa kallon shirye shirye a ɗakunan su kuma masu inganci da ma’ana.

Mene ne saƙonka na ƙarshe?
To saqona shi ne, Ina kira ga waɗanda za su fara yin finafinai na YouTube su yi taka tsantsan, don gaskiyar magana Ina tausayawa duk wanda ya ɗauko kuɗin sa ya zuba, domin a yanzu abubuwan sun yi yawa, duk da cewar ba su yi yawa ba idan ka kalli ƙasashen da suka ci gaba kamar Turkey, za mu ga ba mu kai ko kaso guda cikin ɗari da su suke yi ba, don haka yawan da muke da shi ba yawa ba ne, abin da kawai muke buƙata mutane su sani, fim saƙo ne, don haka kada mutum ya yi tunanin kuɗi da ɗaukaka ta duniya, ya je ya ɗauko abin da shi ba zai yi farin ciki da shi ba, ya zama duk abin da za ka yi a cikin fim ka ɗauke shi a matsayin saƙo da ka ke aikawa kuma za ka yi alfahari da wannan abin idan an nuna shi, sannan za ka iya danganta kan ka da abin a ko’ina ba tare da ka ji kunya ba, kuma mutane su cire kuɗi, don haka ka bi hanya mai kyau wajen aikin ka yadda mutane za su yave ka, kuma kuɗin za su zo daga baya, ka san cewar duk abin da ka yi a matsayin ka na Bahaushe, to harshenka kana vata shi ne ko ka na inganta shi, don haka mu zama wakilai na harshenmu kuma wakilai masu kyau.

To madalla, muna godiya.
Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *