Fintiri ya ƙaddamar da hanyoyi a Adamawa

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya ƙaddamar da hanyoyi na sama da kilomita 340 a sassan jihar da zimmar sauƙaƙa wa ‘yan karkara sha’anin zirga-zirga

Aikin samar da hanyoyin haɗin guiwa ne tsakanin gwamnatin Adamawa da Bankin Duniya da cibiyar French Development Agency ƙarkarshin Shirin Samar wa Karkara Hanyoyi na Gwamnatin Tarayya (RAMP-2).

Hanyoyin da aka aka ƙaddamar sun shafi ƙananan hukumomi 21 da jihar ke da su ne.

Yayin da yake magana a wajen ƙaddamar da hanyoyin, Gwamna Fintiri ya ce gwamnatinsa ba ta sa wasa ba wajen biyan kasonta ga shirin haɗin guiwar wanda hakan ya taimaka wajen samar da hanyoyin da aka ƙaddamar.

Tare da shan alwashin duk wani aiki da gwamnatinsa ta soma aiwatarwa a jihar zai tabbatar da an kammala shi kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa na farko.

Daga nan gwamnan ya yaba wa Bankin Duniya da French Development Agency da sauran ɓangarorin da aka yi haɗaka da su, dangane da rawar da suka taka wajen cim ma nasarar aikin samar da hanyoyin. Haka nan, ya yi alƙawarin ci gaba da yin aiki tare domin bai wa ‘yan jiharsa damar cin ribar dimukraɗiyya yadda ya kamata.

Babban baƙo a wajen taron ƙaddamarwar kuma gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yaba da ƙoƙarin takwaransa wajen inganta fannonin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *