Fintiri ya kere Binani da ƙuri’u 35,617 a ƙananan hukumomi 20 cikin 21 a Adamawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A halin yanzu Gwamna Ahmadu Fintiri kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP ne ke kan gaba da babbar abokiyar hamayyarsa Aishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC da ƙuri’u 35,617.

Wannan dai ya zo ne a sakamakon ƙananan hukumomi 20 cikin 21 na jihar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta bayyana a cibiyar tattara sakamakon zaɓen jihar da ke Yola. Ana dakon sakamakon ƙaranar hukumar Fufure.

Daga cikin ƙananan hukumomi 20 da aka bayyana kawo yanzu, PDP ta samu ƙuri’u a 13, inda ta samu ƙuri’u 401,115, yayin da APC ta samu ƙuri’u a 7 da ƙuri’u 365,498.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *