Firaministan Sin ya jaddada aniyar haɗin gwiwa da ƙasashe masu magana da harshen Portugal

CMG HAUSA

Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya yi kiran a ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashe masu magana da harshen Portugal.

Li ya yi wannan tsokaci ne a yayin da ya halarci bikin buɗe taron musamman na ministoci na dandalin haɗin gwiwar raya tattalin arziki da ciniki na ƙasar Sin da ƙasashe masu magana da harshen Portugal (PSCs), wacce aka fi sani da Forum Macao.

Li ya ƙara da cewa, yawan ciniki a tsakanin ƙasar Sin da ƙasashe masu magana da harshen Portugal, ya zarce dalar Amurka biliyan 100 a shekaru biyar a jere, yayin da adadin ya kai dala biliyan 200 a shekarar da ta gabata, lamarin da ya nuna a fili irin gagarumin ci gaban da aka samu da kuma kyakkyawar makomar haɗin gwiwar ɓangarorin biyu.

A cewar firaministan, ƙasar Sin za ta kara samar da gudunmawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar duniya da kara azama kan ci gaba da samun wadata a ƙasa da ƙasa, ta hanyar haɗa kai da ƙasashe masu magana da harshen Portugal har ma da duniya baki ɗaya.

Li ya ce, ƙasar Sin a shirye take ta kara yin haɗin gwiwa da ƙasashe masu magana da harshen Portugal a fannonin allurar riga-kafi, da magunguna, da kiwon lafiya, da kuma kafa cibiyar musaya wajen yaki da annoba a yankin musamman na Macao na ƙasar Sin.

Firaministan ƙasar Sin ya buƙaci a ƙara yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, ya ce, ƙasar Sin a shirye take ta ƙara inganta haɗin gwiwarta wajen bunƙasa kayayyakin more rayuwa, da masana’antu, da yin tsimin makamashi, da kare muhalli.

Mahalarta taron sun haɗa da wakilan gwamnatin Sin, da na ƙasashe masu magana da harshen Portugal takwas, da suka haɗa da Angola, da Brazil, da Cape Verde, da Guinea-Bissau, da Mozambique, da Portugal, da Sao Tome da Principe, da kuma Timor-Leste.

Mai Fassara: Ahmad