First Bank ya ƙwato rancen biliyan N456 daga bankin Heritage kafin a ƙwace lasisinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bankin First Bank ya samu nasarar karɓo cikakken rancen Naira Biliyan 456 da ya baiwa bankin Heritage, a wani ɓangare na shirin bayar da lamuni a zamanin mulkin tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele.

Majiyoyi a cikin First Bank, da suke magana da Nairametrics, sun bayyana cewa CBN ya baiwa bankin bashin da ake kira ‘tier-one’ kafin ya sanar da soke lasisin bankin Heritage.

Dakatar da bankin, wanda CBN ya sanar a ranar Litinin, ya bada misali da yadda Bankin Heritage ke ci gaba da fama da matsalar kuɗi da kuma rashin samun damar farfaɗowa, wanda a ƙarshe ya kai ga durƙushewarsa.

Ƙwato Naira biliyan 456 ya kawo aarshen ƙoƙarin da aka yi na tsawon shekaru bakwai tun bayan da bankin First Bank ya tallafa wa bankin Heritage wajen warware hada-hadar kasuwanci.

Wannan biyan bashin zai ƙarfafa matsayin bankin First Bank, wanda aka nuna a cikin bayanan kuɗi na FBN Holdings, wanda ke nuna ribar da aka samu kafin harajin Naira biliyan 358.8 da kuma taɓarɓarewar Naira biliyan 227.4.

Ƙalubalen Bankin Heritage ya fara shiga ne a shekarar 2019, wanda ya sa CBN shiga tsakani don hana durƙushewar sa. Duk da tallafin da aka ba shi, matsalar kuɗi ta Bankin Heritage ta cigaba da taɓarɓare, wanda ya kai ga CBN ya yanke shawarar soke lasisin bankin.

Hukumar Inshora ta Nijeriya (NDIC) ce ta fara aiwatar da shirin, inda ta tabbatar da kariyar masu ajiya tare da biyan kuɗi har Naira miliyan 5, ya danganta da abin da suke ajiya.