
Daga BELLO A. BABAJI
A yammacin yau ne fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdu Kano da aka fi sani da Baba Karƙuzu, ya rasu.
Za a yi masa sallar jana’iza a gobe da safe a gidansa da ke Haruna Hadeja Street, a Jos Babban Birnin Jihar Filato.
Allah Ya jiƙan sa Ya kuma gafarta masa tare da bai wa ƴan uwa da abokan arziƙi haƙurin juriyan rashin sa.