Fitaccen tsohon ɗan wasa Fontaine ya rasu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Just Fontaine, wanda ya kafa tarihin zura mafi yawan ƙwallo a raga a gasar kofin duniya ɗaya, ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.

Fontaine ya ci wa Faransa ƙwallaye 13 a wasanni shida kacal a gasar kofin duniya da aka yi a Sweden a shekarar 1958 inda ta zo na uku.

Yana matsayi na huɗu a jerin waɗanda suka fi zura ƙwallaye a gasar kofin duniya tare da Lionel Messi na Argentina.

“Za a kewar tauraron ƙwallon Faransan, fitaccen ɗan wasan gaba, fitaccen ɗan wasan Reims,” in ji tsohon kulob ɗin Stade de Reims.

Wani tsohon kulob ɗinsa, Paris St-Germain, ya ce, “dole a riqa runawa da Just Fontaine. Alamar ƙwallon ƙafa ta Faransa wanda ya bar mu. “

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa (FFF) ta bayyana Fontaine a matsayin “mai cin ƙwallo na gabaɗaya” kuma “babban wanda ya kafa tarihin cin ƙwallo na duniya”.

“Mutuwar Just Fontaine ta jefa ƙwallon Faransa cikin ɗimuwa da tunani da bakin ciki,” in ji shugaban FFF na riƙon kwarya, Philippe Diallo.

“Ya kafa ɗaya daga cikin mafi kyawun tarihi a ƙungiyar Faransa.”

Za a yi tafi na minti ɗaya don girmama Fontaine a dukkan filayen wasan ƙwallon ƙafar Faransa, inda za a fara wasannin ranar Laraba a gasar kofin Faransa.