(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
A satin da ya gabata, mun kawo wasu daga cikin mawaƙan da suka ɗanɗani zaman gidan yari da kuma dalilan da ya kai su. Sannan mun yi ma ku alƙawarin ci gaba da wannan darasi, don samun kawo ƙarin wasu kafin mu rufe darasin.
Shahararrun mawaƙa da suka yi rayuwar gidan kaso na ɗan da dama, don haka ba za mu iya kawo wa masu karatu dukka ba, saboda haka za mu tsakuro ne daga ciki. A sha karatu lafiya.
Burna Boy:
Mawaƙi Burna Boy ba ya buƙatar gabatarwa a wannan zamani musamman ma a tsakin matasa masu tasowa a ciki da wajen Ƙasar Nijeriya. A shekarar 2010 ne aka samu rahoton mawaqin ya shiga komar ‘yan sanda a Amurka, sakamakon daɓa wa wani wuƙa da ya yi.
Yayin da aka kai mawaƙin kotu, ya musanta laifin kamar yadda ake tsamani, duk da haka sun tura shi magarƙama tsayin watanni 11, kafin a yi ma shi afuwa bisa kyawawan hali da ya nuna.
D’Banj:
Mawaqin da za mu iya cewa ya yi ficen da ba kasafai ake iya samun wanda bai san shi ba a Ƙasar Nijeriya. A ƙarshen shekarar 2022, wato a watan Disamba, mawaƙi D’Banji ya shiga komar Hukumar Yaqi da Cin Hanci da Rashawa, wato ICPC.
Hukumar dai ta damƙi mawaƙin ne bayan ta dira gidan sa kan zargin sa da zamba, wanda ya tilastashi bayyana a shalkwatarsu da ke birnin tarayya, Abuja.
Ana zargin mawaƙin da hannu dumu-dumu a zamba da karkatar da miliyoyin Nairori na gwamnatin Nijeriya da aka ware don gudanar da aikin N-Power, a lokacin mawaƙin na matsayin jakada a ma’aikatar.
Rahotanni da dama sun bayyana cewa, mawaƙin ya haɗa kai da wasu ma’aikatan gwamnati wurin shigar da sunayen bugi waɗanda ake biya a asusun da aka alaƙanta shi da mawaƙin.
Portable:
Mawaƙin da a halin yanzu yake jan zaren shi daidai gwargwado Portable, ya shiga komar ‘yan sanda a ranar 31 ga watan Maris, na shekarar nan ta 2023. ‘Yan sandar Jihar Ogun ne suka danƙe mawaƙin bayan da ya qi amsa gayyatar da suka aika mashi da ita.
Mawaƙin ya ƙara zafafa lamarin ta yadda ya dinga jifar jam’ian na ‘yan sanda da kalamai marasa kyau a sa’ilin da suka kawo masa damƙa a mashayarsa da ke Santa Ota da ke Jihar Ogun.
Sanadin kafiyar da ya nuna tare da nunawa jami’an shi wata tsiya ne, ba su isa su kama shi ba ya sa rundunar ‘yan sandan maka shi kotu bisa tuhumar sa da cin zarafi, rashin ɗa’a da kuma satar kayan aikin kiɗa.
Mawaƙin ya zauna a tsare tsayin kwanaki kafin a ranar 3 ga watan Afrilu, alƙalin da ke shari’ar da ke Qaramar Hukumar Ifo ta Jihar Ogun ya bayar da belin sa, bayan ya yi zaman gidan yari na Iloro.
Sinzu:
Rahotanni sun bayyana Sinzu ya shiga hannun hukuma ne a Ƙasar Amurka, a shekara ta 2017, bisa laifin satar sama da Dalar Amurka 15,000 ta hanyar zambar katin banki.
Mawaƙin wanda aka fi sani da Sauce Kid, wanda ya soma harkar waƙa tun a shekara ta 2005, da waƙarsa mai mai suna ‘Omoge Wa Jo’. Mawaƙin da ake hasashen zai iya kai matakin ƙarshe na shahara a waƙa da bai taka birki ba bayan kammala karatunsa na babba makaranta, inda ya kwashe kayanshi ya koma Ƙasar Amurka, wannan ne ya ba wa mawaqa irin su Donjazzy, Dbanji damar zama jan wuya a harkar waƙa.
Bayan komawar mawaƙi Sauce Kid Ƙasar Amurka, waqa ta zama ƙarfi-ƙarfi gare shi, kuma a cikin irin wannan yanayin ne ya faɗa komar ‘yan sanda, da ta kai shi ga zaman gidan kaso na tsayin shekaru biyu.
Dammy Krane:
Labarin kamen mawaƙi Dammy Krane ta bayar da mamaki ga kaso mafi yawa na masoyansa, kasancewar laifin sata da ake zarginsa da shi. A wani vangare za a iya cewa biri ya yi kama da mutum, kasancewar shi mutum mai matuƙar son yin tsadaddiyar rayuwa, wadda ake hasashen ta kai shi ga aikata laifin na sata.
Mawaƙi Dammy wanda cikakken sunansa Oyindamola Johnson Emmanuel ya shiga hannun hukuma ne a ranar 2 ga watan Yuni a shekarar 2017 kan laifin zamba da satar kuxin ATM.
Mawaƙin da ya yi waƙar ‘Ameen’ ya yi amfani da katin ATM da ya sata wurin hayar jirgi don yin tafiya shi kaɗai, wato private jet, wanda jami’ai suka yi amfani da kamfanin wurin damƙar shi.
Ya yi zaman gidan kaso na kwanaki uku zaman jiran zaman kotu, kasancewar ya musanta dukka zargin da ake yi masa. Bayan sake zaman, kotu ta yi watsi da dukka tume-tumen da ake yi wa mawaƙin, kuma ta bada umurnin sallamar sa.