Fitattun mawaƙan Nijeriya da suka taɓa zaman gidan kaso

Daga AISHA ASAS

Sau da dama shahara kan ruɗi wasu daga cikin masu tare da ita, har su fara tunanin za su aikata kowanne irin laifi su sha. Sukan ruɗu da cewa, ƙasarsu cike ta ke da masoyansu wanda za su iya samun alfarma ta kowanne ɓangare. Da wannan ne suke ganin taka doka bai zama wani babban lamari a wurin su ba.

Wasu kuwa ba wannan tunanin ne ke aika su ƙa saɓa wa doka ba, giyar ɗaukaka ce da suka ɗirka ta bugar da su, ta hana su tunanin makomarsu yayin da suka hasala hukuma. Don haka sai su yi ta tsula tsiyar su hankali kwance.

Hakazalika akan samu waɗanda suke mutanen ƙwarai sosai kafin nasara ta ƙwanƙwasa musu ƙofa, amma da zaran sun zama wata tsiya sai su ari halayen sababbin mutanen da suka shigo rayuwarsu a lokacin na ɗaukan.

A wani ɓangare kuwa, ɗaukaka kan yi sanadin samun ƙarin maƙiya, da samun yawaitar gadar zare da tugu da makirci da maƙiya za su dinga shiryawa a ƙoƙarin ganin sun mayar da kai baya, don haka takan yiwu a shirya abinda zai iya kai ka ga fushin hukuma ba tare da ka aikata laifi ba.

Da wannan ne wasu ke sanya wannan a layin ɗaya daga cikin ƙalubalen da shahara ke zuwa da shi. Kuma sau da yawa ba su cika farga ba har sai halayyan sun masu dabaibayin da suka kasa ƙwatar kansu.

Idan muka ce mu ɗora alhakin munanan ɗabi’u da ake samu a tsakanin mawaƙa ko masu harkar fim kan raunin hukunta masu laifi da yawaitar cin hanci da rashawa da ya yi wa ƙasarmu kamun kazar kuku, tabbas ba a yi adalci ba, duba da cewa a ƙasashen da muke kallo da sha’awa kan bin doka da oda ma akan samu irin wannan a cikinsu.

Idan mun ɗauki Ƙasar Amurka a misali, mawaƙa da dama sun yi zaman kaso kan wasu laifuka kamar na ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, cin zarafin mata, mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba da makarantansu, kuma wannan bai tsaya iya mawaƙa ba, za ka iya samu a jarumai ko wasu shirya finafinai da sauran harkokin na nishaɗantarwa. Mawaƙi R. Kelly na ɗaya daga cikin misalan da za mu iya bayarwa.

Kuma idan ba mu manta ba, a baya-bayan nan aka kama ɗan fitaccen jarumi a masana’atar finafinai ta Indiya, Shah Rukh Khan kan zargin ta’ammali da ƙwaya, wanda hakan ya tada ƙura a masana’antar da ta yi sanadiyyar tonon silali da wasu da yawa suka yi wa wa’ansu, na irin halin da shahara ta jefa su, har wata ta ke iƙirarin duk wani jarumin da ya amsa sunanshi a masana’antar idan ya shirya wani biki na manyan fitattun jarumai irinsa dole ƙwaya tana cikin ababen da za a samu a wurin taron.

Da wannan ne shafin Nishaɗi na jaridar Manhaja ya yi shiri don kowa wa masu karatu wasu daga cikin manyan mawaƙa da suka karya doka da har ta kai su ka zaman gidan yari:

Fela Anikulapo Kuti:

Kusan kaso mafi rinjaye sun san fitaccen mawaƙi da ya kafa tarihi a fannin waƙa, wato Fela. Waƙoƙinsa sun zama game gari a tsakanin mutanen da ke jin yaren da yake amfani da shi da ma masu son waƙoƙin don ƙwarewar sa.

A shekarar 1984 ne ‘yan sanda suka cika hannu da fitaccen mawaqin da ya yi ƙaurin suna wurin faɗar zahiri na al’aurran yau da kullum a waƙoƙinsa, a lokacin tsohon shugaban ɗasa, Muhammadu Buhari na mulkinsa na farko a ƙarƙashin mulkin soja.

An tambatar da an kama shi ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, a lokacin da yake yunqurin barin ƙasa da zummar yin wasa a Turai.

A wannan tafiya ne, ma’aikatan filin jirgin suka kama mawaƙin da tsabar kuɗin Birtaniya har fawun 1,600, kuma a lokacin gwamnati ta shar’anta dokar kama duk wanda aka kama da kuɗin da suka haura fawun 500.

Duk da cewa, mawaƙin ya yi ƙoƙarin lurar da su kuɗin ba iya nasa ba ne, har da jama’arsa waɗanda suke tare da shi a harkar waƙar, kuma adadinsu ya kai 26, sai dai duk da hakan sai da ‘yan sanda suka yi ram da shi.

Wannan bayani na Fela bai yi tasiri ba a kotu, domin bai hana a yanke masa hukuncin zama gidan kaso na tsayin shekaru goma ba. Sai dai ya yi zaman kaso na watanni 20 ne, wato shekara ɗaya da wata takwas kafin ya shaƙi iskan ‘yanci a daidai lokacin da aka hamɗarar da gwamnatin Muhammadu Buhari.

A lokacin da mawaƙi Fela ya fito daga gidan kaso, ya tattauna da manema labarai inda yake cewa, “gidan maza bai canza min rayuwa ba, sai dai ya ƙara min kaifin tunani tare da ba ni loacin hangen nesa kan lamarin duniya da yadda ta ke tafiya, ya sanar da ni ma’anar lokaci da yadda za ka iya cin moriyarsa.

Ba na tunanin waƙa a lokacin da nake cikin gidan kaso, sai ɗan wani lokaci kaɗan da waƙar ke zo min, sai dai ban yi yunqurin rubuta ta ba. zaman da na yi bai kasance wasa gare ni ba, don haka ban cika magana ba, kuma Ina ƙoƙarin nisanta kaina da mutane da sha’aninsu.

Dama dai maƙasudin kafa gidan yari don ya sa ka a kaɗaici mai tarin yawa ne, ta yadda gobe za ka yi fargaban komawa kan abinda ya kawo ka wurin a baya. Don haka na ce, kuna so ne in shiga kaɗaici, don haka na koyi kaɗaicin kuma na mayar da shi jiki, don gobe kada ya zama barazana gare ni idan na sake dawowa. Zan iya cewa ma wuri ne da na koyo haƙuri, dama na je wurin ne don na koyi kaɗaici, kuma na koya, don haka a shirye nake da komawa a duk lokacin da ta kama.”

Naira Marley:

Ɗaya daga cikin manyan mawaƙan da suka samu kansu a magarƙama akwai fitaccen mawali Naira Marley. Lamarin ya samo asalinsa ne tun a lokacin da ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Instagram, rubutun da za a iya kira da hanya ta bayyana abinda ya dangace shi.

Mawaƙin ya bayyana cewa, damfarar yanar gizo ba lafi ba ce, hukunta fararen fata ne kan azabtarwar da suka yi wa kakaninmu. Wannan rubutu nasa ya ja ƙura a lokacin wanda hakan ya sa aka yi kansa da kalaman ƙolarin gyara ko canza ra’ayinsa, sai dai mawalin ya tsaya ƙyam kan furucinsa da kuma abinda ya qunsa.

A ƙoƙarin ƙara tabatar wa duniya ra’ayin nasa kan damfarar yanar gizo, mawaƙin ya haɗa kai da abokin waƙarsa kuma amininsa Zlatan suka saki zafaffiyar waƙa da ke magana kan damfarar, wadda suka sanya wa suna ‘Am I A Yahoo Boy”.

A ranar 10 ga watan Mayu, sheakarar 2019, Hukumar EFCC ta damqi mawaƙi Naira Marley tare da abokinsa Zlatan da kuma Rahman Jago da wasu abokanin nasu biyu kan zargin damfara da kuma halasta kuɗin haram, wato money laundry.

Kwanaki biyar bayan wannan kame, Zlatan, Rahman Jago da sauran biyu suka shaƙi iskan ‘yanci, yayin da suka bar mawaƙi Naira Marley a can. Wannan na nufin shi ne bincikensu ya nuna a matsayin mai laifi, kasancewar an samu sheda a komfutarshi da zai tabbatar da hannunsa dumu-dumu a laifin da ake zarginsa da shi.

Take hukumar ta miƙa shi a Babbar Kotun Ikoyi da ke Jihar Legas, inda ya musanta duk laifukan da ake tuhumar sa da su, don haka kotu ta ɗage zaman zuwa ranar 30 ga watan na Mayu, hakan ya sa aka koma da shi gidan maza jiran ranar.

Bayan dawo wa kotun ne aka yi nasarar samun belin mawaƙin akan kuɗi Naira miliyan biyu, bisa sharaɗin halartar kotu a ranar da za a sake zama, wato a watan Oktoba.

Za mu ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *