Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Gaskiya ne an shiga kakar siyasar zaɓen 2023 a Nijeriya inda kullum za aka iya jin sabon abu kama daga batun sauya sheƙa, fitowar ‘yan takara, caccakar juna da ma batun Kudu da Arewa. Kuma ai ma abin da ya fi ɗaukar hankali zuwa yanzu shi ne zare Naira miliyan 100 don sayen fom ɗin neman tikitin takarar shugabancin Nijeriya a inuwar jam’iyyar APC mai gwamnatin taraiya. Tun da a ke a tarihin siyasar Nijeriya ba a taɓa samun fom mai tsadar wannan ba.
Kazalika hakan ma ya fito a jam’iyya mai mallakar shugaba Buhari wanda ke kokawa kan yawan kuɗin fom ɗin takara a lokutan da ya tsaya takara a baya kafin ya dare madafun iko a 2015. Majalisar ƙoli ta APC ta gudanar da taro ta ayyana fom ɗin takarar Naira miliayn 100 amma ba a ji wani ya yi tari ko ya ce a’a ba daidai ba ne don ba wai lalle sai mutum ya na mallakar maƙudan kuɗi ne zai cacncanci tsayawa takarar shugabanci ba.
Abin lura duk da wannan ƙalubale na yawan kuɗin, duk wanda ka ga ya sayi fom ɗin takarar nan Naira miliyan 100 to ba mamaki ya na da Naira biliyan ɗaya ko ma biliyoyin Naira da ma dalar Amurka da Fam ɗin Ingila da Yuro na tarayyar Turai. Bayan zaɓen fidda gwani mutum ɗaya ne tak zai lashe zaɓen cikin waɗanda su ka miqa wannan zunzurutun kuɗi ga jam’iyya.
Ba nan ne cacar siyasa ba, don wani zai iya kashe kuɗin don kawai a ce a tarihi ya taɓa zama mai neman tikitin takara. Wani zai yi haka don in an zo damawa a gwamnati in Allah ya sa a ka yi nasara a dama da shi. Mai mukamin minister ya samu mai kwangila ya samu mai tura mutanen sa a ba su ayyuka ko muƙamai ya tura. Babban abu zai iya zama yana daga cikin kwamitin amintattu na jam’iyyar sa! To me ya rasa tun da komai da shi za a riƙa yi.
Ka ga zuba jari ne ko adashen da a kan ci riba ninkin-ba-ninkin. Ba mamaki shigowar gwamnatin shugaba Buhari a 2015, ta rage yadda a kan saka wa waɗanda su ka yi wa jam’iyya hidima, amma duk da haka akwai da dama da su ka shiga gwamnati kai tsaye ko ta wata hanyar wasu da su ka lura da gudunmawar da su ka bayar. An ruwaito sabon shugaban APC Sanata Abdullahi Adamu na cewa neman zama shugaban Nijeriya ba kamar mutum ya nemi zama sarkin ƙauyen su ba ne, don haka duk wanda ba zai iya samun waɗanda za su tara ma sa Naira miliyan 100 ba, bai cancanci ya tsaya takarar ba. Sanata Adamu ya ƙara da cewa, shi kan sa sai da ya biya Naira miliyan 20 lokacin da zai tsaya takarar shugabancin APC inda waɗanda su ka gabace su, su ka biya Naira dubu 500.
Sabon shugaban na APC ba a nan ya tsaya ba, ya ce sanya Naira miliyan 100 ga takarar hikimar ture shaiɗanu ne da ka iya sayawa wasu fom ɗin su shiga takarar don batawa jam’iyyar harka. Adamu ya ce za a ga mai son bata ruwan da zai iya sayawa wani fom ɗin kan waɗannan maƙudan kuɗin. Mutane sun nuna mamakin yawan kuɗin da irin yadda jam’iyyar ke cewa ba a wani abin tada jijiyar wuya ba ne.
A zaɓen fidda gwani na APC a 2015 shugaba Buhari ya nuna damuwa kan kuɗin fom ɗin Naira miliyan 27 inda ya ke cewa bai san yaya kalar wannan fom ɗin mai tsada zai bayyana ba. Da ma a ce kuɗin fom ɗin ne kaɗai logar lashe zaɓe ko daga nan sai shiga zaɓe da kuwa da sauƙi.
Amma yanzu akwai batun zaɓen zai gudana ne ƙarƙashin wakilai daga jihohi. A bisa al’ada akwai hidima mai yawa da a kan yi wa wakilan da sai mai irin waɗancan maƙudan kuɗi ne zai iya shiga ruwan ya fit aba da kiran habu ba. Don haka in kun tuna ai sai da shugaba Buhari ya fitar da tsarin kankare kati da mai Naira 100 zuwa sama zai tura don taimaka ma sa ɗaukar nauyin kamfen.
A 2019 ma ya na kan kujerar wasu ne su ka yi wuf su ka sayawa shugaban fom ɗin. Wai duk wannan fa ga shugaba Buhari da ba ya ba wa magoya bayan sa ko sisin kobo don su fito kare ma sa ƙuri’a. Alamu na nuna yadda mutane su ka ji jiki da shiga quncin talauci, zai yi wuya su biyewa yi wa ‘yan siyasa hidima a na Bello-Badun ko a fayu. Kaunar takarar shugaba Buhari daga 2003-2015 ya sa masu zaɓe musamman a arewacin Nijeriya daina maƙala ganye a kunnen su don neman a saye su su kaɗawa mai kuɗi ƙuri’a.
Maimakon ma sanya ganye, mutane kan fitar da kuɗi daga aljihun su da ma sayen ruwan sha har da abinci don kar wani ya sauya ƙuri’ar shugaba Buhari. Jama’a ina fatan kun tuna logar siyasar nan da shugaba Buhari ya kawo ‘APC SAK’ daga bisani ya inganta logar zuwa ‘JIKI MAGAYI’ inda daga ƙarshe ya kawo ta kankat wato ‘A KASA A TSARE’ da a ka yi amfani da shi a ka yi kare jini biri jini a 2011 inda a 2015 a ka kawar da PDP daga fadar Aso Rock.
Abin da za a duba shi ne mutane na fatar a samu wani tsari da talakawa ne za su karɓi ragamar shugabancin su da kan su. Don kuwa ai talakawa ne su ka fi yawa a ƙasar nan. Kazalika a samu yanayin da ƙuri’ar talaka ce za ta yi aiki tun daga kan zaɓen fidda gwani zuwa zaɓen gama-gari. Duk wannan tunanin bai tabbata ba don kuwa a zaɓen fidda gwani na ƙarƙashin wasu wakilai ne ƙalilan da ba lalle talakawa ne su ka canko su don zaƙulo gwanin ba.
Akwai zargin yadda mafi yawan kuɗi shi ke iya mallakar nasara daga wajen wakilan. In ma mutum bai yi magana kai tsaye da wakilan ba, ya zama wajibi ya samu goyon bayan gwamnoni da ke da tagomashin samun biyar da wakilan. Samun goyon bayan gwamnonin jam’iyya gagarumin aiki ne da sai ko wanda ya ke kan kujerar gwamna ko wanda ya taɓa yin gwamna ko wanda fadar tarayya ta marawa baya da nema ma sa goyon bayan gwamnonin kamar yadda ya faru lokacin da Obasanjo ya canko marigayi Umaru ’Yar’adua ya zama dan takarar PDP a 2007.
Shugaba Buhari ya nuna ba shi da sha’wa ta kai tsaye ya bayyana wanda ya ke marawa baya. A ra’ayinsa bayyana wanda ya ke son ya karɓi mulki a hannun sa tamkar neman a ƙulla maƙarƙashiya ne ga mutumin inda za a iya gamawa da shi kafin lokacin zaɓen. Idan har shugaban bai nuna wanda ya ke so ya zama gwanin sa ba, haƙiƙa gwamnoni za su zauna su fito da wanda su ke ganin zai kare muradunsu, su sama ma sa wakilai ya lashe zaɓen.
Wani bayanannan lamari shi ne ba lalle ne ko ɗan takara ya yi amfani da kuɗi wajen alheri ga wakilan ba zai samu goyon bayan su a zaɓen fidda gwani. Babban abu samun goyon bayan gwamnoni da su ke mallakar wakilan shi ne mafi zama dahir. A nan ba iya cewa shugaba Buhari ba zai fito da dan takarar sa ba ko da ta bayan fage ne don yadda lamarin ya kasance a zaven shugaban APC. Tun a na ɗaukar lamarin cankar Abdullahi Adamu a matsayin shaci-faɗi har abin ya tabbata cewa shugaban ne ke son ya zama shugaban APC.
An fahimci cewa fadar Aso Rock na buƙatar Adamu ne don tsohon gwamna ne a jihar Nassarawa kuma ya taho majalisar dattawa kazalika ga yawan shekaru, don haka ba zai lamunta da gwamnoni su murda lamuran zaven cikin gida na jam’iyya ba. Duk da haka za a iya cewa a APC Abdullahi Adamu ne kai tsaye ɗan takarar shugaba Buhari, sauran shugabannin jam’iyyar sun fito ne bisa yarjejeniyar gwamnoni. Ya nuna gwamnoni na da manyan wakilan a majalisar gudanarwar jam’iyyar. Wannan zai sa in lamura su ka rincave a samu gwamnoni sun fito sun nuna hanyar da za a bi.
Tun shigowa kakar zaɓen 2023 mu ke jin wasu na cewa guguwar shugaba Buhari ta kare don haka ko shugaba Buhari ya daga hannun ɗan takara ba lalle ne ya lashe zaɓe ba. Koma dai yaya za a ce za mu jira in Allah ya sa da sauran numfashi mu ga yadda za ta kaya tsakanin shugaba Buhari, masu tasiri a gwamnatin sa da ke yi wa taken ‘CABAL’ da kuma gwamnoni masu kuɗi da wakilai.
Kammalawa:
Yayin da APC ke shirin gudanar da zaven fidda gwanin a ƙarshen watan Mayun nan, ita ma babbar jam’iyyar adawa ta PDP tana irin wannan shiri da zuwa yanzu ta ke da ’yan takara 17 tsakanin mutan Kudu da Arewa. PDP ta lashi takobin kawar da APC da ta ce ba ta taɓukawa talakawa abin kirki ba. Jama’a masu kaɗa ƙuri’a su ne alƙalai bisa bayanan hukumar zaɓe.