Daga UMAR GARBA a Katsina
A makon da ya gabata ne aka riƙa yaɗa wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka ga ɗaliban jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsimma a Katsina sun hau wata babbar motar dakon man fetur a hanyarsu ta zuwa jami’ar.
Saboda haka ne hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) ta buƙaci jami’ar da ta ƙara ƙaimi wajen samar da isassun motocin bas da za su kai ɗalibai daga tshohuwar harabar makarantar zuwa sabon mazaunin jami’ar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kwamandan hukumar FRSC, Aliyu Ma’aji ya fitar ta hannun mai magana da yawun rundunar, Shamsudeen Babajo, a Katsina.
Ma’aji ya ce hukumar ta FRSC ta yi Allah wadai da yadda ake amfani da manyan motoci da tireloli wajen kai ɗaliban makarantar daga masaukan ɗaliban zuwa sabon mazaunin jami’ar.
“Muna kira ga hukumar makarantar da ta gaggauta gyara motocin bas ɗin makarantar,” in ji shi.
Ya ce, rundunar ta shirya wata tawaga ta musamman tare da haɗin guiwar sashin Ko ta kwanaa na FRSC domin gudanar da sintiri domin tabbatar da bin doka da oda, yana mai gargaɗin cewa irin wannan muguwar ɗabi’ar na iya janyo asarar rayuka.
Da yake mayar da martani kan batun, kakakin jami’ar, Nasir Abdul, ya ce jami’ar ta samar da isassun motocin bas da za su yi jigilar ɗalibai zuwa jami’ar.
“Hukumar makarantar ta samar da isassun motocin bas da isassun mai domin safarar ɗaliban.
“Shugaban jami’ar ya damu da jin daɗin ɗaliban jami’ar. Ba zan iya cewa ba mu da masaniya game da irin waɗannan labarai ba. Yawancin ɗaliban ana kai su ne a cikin motocin bas na makaranta tare da jami’an tsaro saboda matsalar tsaro,” in ji Mista Abdul.
A cewarsa, ɗaliban da aka gani a cikin motar su ne waɗanda suka ƙi jiran motocin bas ɗin makarantar don a kai su cikin jami’ar.
“Mun damu da halayen irin waɗannan ɗaliban saboda mun samar musu da isassun motocin bas,” in ji shi.