Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wakilan jam’iyyar adawa ta PDP sun fice daga babban zauren karɓar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ke gudana a Abuja.
An dai ce Sanata Dino Melaye ya haɗa wakilan jam’iyyar domin gudanar da taron gangamin idan har hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) bata yi biyayya ga ƙudirin nasu ba.
Idan dai za a iya tunawa, lamarin ya faro ne a lokacin da Dino Melaye ya yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen jihar Ekiti da aka sanar da farko a ranar Lahadi.
Melaye, wakilin mai riƙe da tutar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya haifar da cece-kuce a lokacin da ya yi kakkausar suka kan cewa shugaban INEC, Mahmood Yakubu ba zai amince da sakamakon zaɓen Ekiti ba, yana mai zargin cewa an tabka maguɗin zaɓe da kuma kura-kurai a zaɓen.