Ƙarancin alburushi ya sa ‘yan sanda yi wa Matawalle ihu a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

‘Yan bindiga sun kashe wasu ‘yan sanda su 14 waɗanda aka girke a Magami a yankin ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara domin yaƙi da harkokin ‘yan fashin daji.

Bayanan wasu daga cikin ‘yan sandan da suka tsallake rijiya da baya a lokacin ɗauki-ba-daɗin, sun nuna an shafe kusan awa guda ana musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindigar kafin daga bisani bindigogin ‘yan sanda suka koma tamkar sanduna a hannunsu sakamakon ƙarewar alburusai.

Sun ce ganin halin da suka tsinci kansu sai suka aika da saƙon gaggawa a kan a sanar da gwamna halin da suke ciki wanda a cewasru lallai saƙon ya isa gare shi kuma a kan kari.

Amma duk da haka babu wani ɗauki da aka kai musu, ba a tura musu ƙarin jami’ai ba balle kuma su samu ƙarin alburusai, lamarin da ya sa da yawan jami’an suka yanke shawarar tserewa don su tsira da ransu.

Tare da cewa jami’ai 14 da suka rasa rayukansu yayin harin, hakan ya faru ne sakamakon ƙarewar alburusai, kuma an kai gawarwakinsu an ajiye a wata asibitin gwamnati da ke Gusau.

Wannan lamari ya fusata sauran jami’an inda aka ga ɓacin rai a fuskokinsu yayin da Gwamna Matawalle ya ziyarci asibitin a yammacin Lahadi. Jami’an sun furta kalmomin ɓacin rai ga gwamnan tare da danganta akasin da aka samu da rashin kulawa daga gwamnan.

‘yan sandan sun yi ƙorafin cewa sama da watanni bakwai kenan ba a biya su alawus ba, sannan babu wani nau’i na gudunmawa da suke samu daga gwamnatin jihar, hatta ƙarin alburusan da za su taimaka musu wajen aikinsu babu.

An yi zargin cewa rashin kulawa da fannin tsaro da gwamnatin Matawalle ke yi shi ke ta’azzara matsalar tsaro a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *