Daga AISHA ASAS
Maiƙo a fuska ba ɓoyayen abu ba ne musamman ga mata. A lokacin da ki ka fahimci fuskarki na ƙyali fiye da adadin yanda ki ka shafa ma ta mai, za ki tabbatar da fuskarki na cikin layin fuskokin da ake cewa ‘oily face’ inji bature.
A wannan sati da yardar Allah shafin kwalliya na jaridar Manhaja zai kawo wa masu bibiyar mu ababen da ke janyo maiƙon fuska da hanyar magance su.
Idan kin gyara mu shiga cikin darasin kai tsaye:
Ana samun fata mai maiƙo ta sanadiyyar yawan fitar ‘sebun’wanda ke ƙarƙashin ikon sabashiyos gilans (sebaceous glands) waɗanda ake samu a ƙarƙashin fata.
shi wannan sinadari na sibon an halitta shi don ya hana fata bushewar da za ta illata ta. Wannan sinadarin ne idan ya yawaita zai kawo maiqo da zai iya damun mai shi.
Me ke janyo maiƙon fuska?
Halittar jini ko kuma ince masarrafar ƙwayoyin halitta wato abin da bature ke kira ‘genetic’: Maiƙon fuska abu ne da za a iya gada daga ɗaya daga cikin iyaye. Idan har ya kasance uwa ko uba na tattare da sabashiyos gilan wanda ke aiki fiye da yanda ake buƙata.
Yawaitar shekaru: a lokacin da ki ke ƙara shekaru, kana samun raguwan sinadarin sibon a jiki wanda ke kawo bushewar jiki ga tsofafi.
Ramen gashi mai girma: wani lokaci matsirar gashi da ke jikin fatarmu kan ƙara girma ta sanadiyar shekaru ko ƙara ƙiba da ragewa. Girman ramen gashi na janyo yawaitar sinadarin sibon.
Kuma uwar gida ta sani ba za ki iya mayar da ramen gashi ƙarami ba, sai dai za ki iya kula da gefen fatar ki da ke da manyar ramuka ta hanyar busar da su ta amfani da abu mai tsotse matsƙi kamar tawul da tissue.