Gadauniyar FLONY ta koyar mata 300 sana’o’i a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gidauniyar Free Light of Nigeria Youth Foundation, wato FLONY a taƙaice, ta yaye ɗalibai mata sama da 300 da aka koya masu  sana’o’in dogaro da kai kyauta.

Taron wanda ya gudana a ofishin Hisba Islamic Centre da ke Rijiyar Lemu cikin birnin Kano, tun da farko a  jawabinsa, shugaban ƙungiyar na Jihar Kano, Mudassir Isyaku, ya ce, an yi mako guda ana koyar da matasa waɗannan sana’o’i da suka haɗa da jakar hannu, man shafawa, kwalliya, turare, sabulu, matasai na zamani da sauransu. Ya kuma yaba da irin namijin ƙoƙari da Sarauniyar Giere ta yi na tsallakowa tun daga Yola, Babban Birnin Jihar Adamawa, ta zo Kano, domin ta horar da mata kyauta.

Sannan ya yi albishir ga Kanawa cewa, nan ba dadewa ba, ƙungiyar ta FLONY za ta sake horar da wasu matan a Jihar Kano.

A jawabinta, shugabar ƙungiyar ta ƙasa kuma wacce ta assasa ƙungiyar, Hajiya Farida Musa Jauro, Tauraruwar Gerie (Uwar Marayu) ta ce, wannan ƙungiya ta koyar da sana’o’i a jihohin Adamawa, Kebbi, Kaduna, Nasarawa da kuma Kano, sannan akwai kuma ƙasashen Nijar da Kamaru.

Ta ƙara cewa, saboda muhimmancin riƙe sana’a ga mata ne ya sanya suka ɗauki mata, don ta koyar da su waɗannan muhimman sana’o’i.

“Domin idan mace ta riƙe sana’ar hannu, to babu shakka al’umma za su amfana da wannan sana’a,”inji ta, sannan ta yi kira da matan da aka koyar da su jajirce su ga  sana’ar ta ɗore har bayan ransu.

Hajiya Farida ta kuma  yaba matuƙa da al’ummar Kano dangane da gudunmawa da suka bayar, musamman har aikin ya yi nasara.

Shi ma a jawabinsa, Sakataren Ƙungiyar, Abdulrahem Adamu Salihu, ya ce, an ƙirƙiri gidauniyar ne a shekarar 2020, wanda daga lokacin zuwa yau wannan ƙungiya ta horar da mata da matasa 11,503 hikimar sana’o’i daban-daban a faɗin ƙasar.

Abdulrahem ya ƙara da cewa, “Hajiya Farida ba a koyar da sana’o’i kaɗai ta tsaya ba, akwai gurare da ta kebe ta ke tallafa wa marayu, sannan tana tallafa wa ɗalibai wajen biyan kuɗin makaranta da sauran ayyukan jinƙai.”

Taron dai ya samu halartar Shugaban Hisba na Kano da Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge da jarumin Kannywood, Adam A. Zango, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ta Flony da sauran jama’a maza da mata.