Gamayyar Ƙasashen Turai za ta maye gurbin amfani da gas ɗin Rasha da na Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

a yayin da ake tsaka da yaƙin Yukiren da Rasha, Gamayyar Ƙasashen Turai (EU) ta sanar da dakatar da shigo da gas daga ƙasar Rasha, inda ta bayyana cewa, za ta dawo harkar cinikin gas ɗin da Nijeriya.

Mataimakin darakta janar na sashen kula da makamashi na kwamitin Gamayyar Ƙasashen Turai, Matthew Balwdin, ya ce ya zo ƙasar Nijeriya a ƙarshen makon da ya gabata, inda ya gana da manyan jami’an ƙasar.

Ya ƙara da cewa, an shaida masa cewa, Najeriya na ƙarfafa tsaro a yankin Neja Delta, inda a can ne ake samar da fetur din.

Jami’an Nijeriya sun gaya masa cewa, an sake buɗe bututun gas da yake tasowa daga kudu zuwa Arewa, wanda zai taimaka wajen faɗaɗa fitar da gas zuwa Turai.

A yanzu haka dai, EU na samun kaso 14 cikin 100 na iskar gas dinta daga Nijeriya, amma akwai alamun yawan zai nunka, kamar yadda Mr Baldwin ya shaida wa manema labarai.

Wannan sabuwar shawara da EU ta yanke tana daga cikin irin yunƙurin da ƙasashen yammacin Duniya sukebyi don ganin sun ƙaƙaba wa ƙasar Rasha takunkumai kan fetur da gas ɗinta saboda kutsen da ta yi wa ƙasar Yukiren.