Game da juyin mulkin ƙasar Nijar

Daga RAHMA ABDULMAJID

A yayin da kwanakin wa’adin ECOWAS ke ƙara ƙaratowa roƙo ɗaya da zan yi wa mahukuntan ECOWAS shi ne, kada su kai hari kan masu juyin mulkin duba da abubuwa uku

  1. Na farko dai, mutanen Nijar din sun ji sun gani, don haka a ƙyale su da zavinsu.
  2. Na biyu, kuɗaɗe da albarkatu da rayukan da ECOWAS din za ta yi amfani da su wajen kai harin, ta yi amfani da su wajen tsaurara tsaro a bodojinta.
  3. Na uku, ƙasashen ECOWAS aminan Rasha ne don haka juyin mulkin Nijar bai kai girman da zai sa waɗannan aasashen su rasa wannan ƙawancen ba.

A maimakon kai harin, ya kamata su yi waɗannan abubuwan:

  1. A tsaurara takunkumi a kan Nijar din tunda sun ce sun ji sun gani. Hasali ma wutan da Najeriya ta janye a jihohi uku mun samu mun yi amfani da shi a cikin gida, hakan na nufin mabuƙatan abinda za ku kashe a Nijar din suna da yawa.
  2. A bar ‘yan Nijar su fahimci mulkin soja a wannan sabon karnin da tauye wa mutum fadin albarkacin baki kadai da mulkin soja kan iya yi ya ishe shi daurin rai da rai, don da alama akwai matasa da yawa da ba su san jiya ba kamar yadda mu ma a nan Najeriya muke da su jibge.
  3. A tsaurara tattaunawa saboda hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar, idan sun fahimci gaskiya ta wajen tattaunawar za a ji a taya su ceton kansu.

Ku kuma ‘yan uwanmu na Nijar ina so ku kwantar da hankalinku ku fahimci wasu abubuwa kamar haka:

  1. Hankalin da ‘yan Afrika ke tayarwa musamman Nijeriya ba ƙiyayya ba ce, son ku ake da jiye muku tsoron abubuwan da muke hangowa ba wanda muke fata ba. Amma idan kun ga hakan ya fi muku, sai mu ce mai ɗaki shi ya san inda dakinsa ke yoyo. Watakil kun fi mu hango hanya mai ɓullewa ne.
  2. Juyin Mulki a Mali da Burkina Faso har zuwa yau bai sauya komai ba, domin abinda suka yi ikirarin kawarwa shi ne, masu jihadin tsattsauran ra’ayi, amma har yau ana nan jiya i yau, iyaka dai an samu ƙarin matakan hana mutanen ƙasar sakat.
  3. Mahukuntan da ke da boda da ku dole su shiga damuwa domin a yayin da suke fama da kansu idan rashin tsaro ya qara ta’azzara a yankinku dole su kara shiga barazana. Don haka, duk so so ne amma son kai ya fi, don haka kada ku zaci za su zuba ido gawa ta yi hatsarin mota.

A ƙarshe Allah Ya sa hakan ya zame mana mafi alhairi bakiɗaya.

Rahma Abdulmajid mai sharhi ce kan lamurran yau da kullum. Ta rubuto daga Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *