GAMJIK 2022: Yadda marubutan adabi suka ɗaura ɗamarar yaƙi da rubutun batsa

Na samu gayyata ta musamman daga ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Kano wato GAMJIK ta hannun abokina kuma marubuci Mansur Usman Sufi, bayan gayyatar da aka yi wa wasu ƙungiyoyin marubuta da nake jagoran ta, waɗanda kuma har wa yau suna daga cikin ƙungiyoyin da suka shiga Gasar Muhawara da GAMJIK ta shirya, domin ƙara ƙarfafa zumunci a tsakanin marubutan adabin Hausa, da ba da gudunmawa a ɓangarorin cigaban rayuwa.

Babu shakka taro ya ƙayatar sosai, kuma an gudanar da shi cikin nasara, saboda yadda aka samu halartar dandazon marubuta daga sassan arewacin ƙasar nan, tsofaffin marubuta, matasa masu tasowa, manazarta harshen Hausa da ‘yan jarida.

An yi zumunci sosai, musamman yadda wasu marubuta suka haɗu da juna ana ta raha, kasancewar wasu da ba a gari ɗaya ake ba, sai dai a haɗu ta zaurukan sada zumunta ana musanyen ilimi da muhawara.

Nima a wajen wannan taro na gamu da wasu sabbin fuskoki da na daɗe ina burin ganin su ido da ido, sakamakon yadda na daɗe ina bibiyar rubuce-rubucen su da gudunmawar da suke bayarwa a harkar cigaban rubutun adabi.

A wannan makon ina ɗauke ne da wata tsaraba da na samo muku daga abubuwan da suka ja hankalina a taron na GAMJIK, wacce tun makon jiya naso fitar, amma saboda wasu dalilai hakan bai yiwu ba.

Wannan tsaraba kuwa ita ce ta yaƙin da marubutan suka ce sun ɗaura ɗamarar yi da marubutan batsa, waɗanda ake kira da marubuta adabin bariki, da nufin tsaftace harkar rubuce-rubucen Hausa daga masu ƙoƙarin ɓata musu suna, waɗanda su ma ‘yan uwan su ne marubuta, amma saboda wasu dalilai suka zaɓi wannan salo wajen isar da nasu saƙonnin.

Salon da akasarin marubuta da masu karatun littattafan Hausa ke ganin yana ɓata tarbiyya, yana kuma zubar da kimar marubutan, da yawancinsu yanzu iyaye ne ko kuma wakilan al’umma, da duniya ke kallo da martaba.

Ko da ya ke ba sai a yanzu ne wasu ke yi wa marubutan adabi kallon suna lalata tarbiyya ba, tun shekaru da dama da suka gabata, wasu daga cikin al’umma ke kallon marubutan littattafan soyayya a matsayin masu ɓata tarbiyyar matasa, wanda ya haifar da buɗe sashi na musamman mai kula da rubuce-rubucen adabi da tallace-tallace, ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, domin sa ido da rage irin kurakuran da a wancan lokacin ake ganin marubuta na yi.

Bayan wasu shekaru ana gwagwarmaya da ba da gudunmawa don samar da sauye-sauye da ƙara wa juna sani, waccan muhawara ta sake dawowa, a wannan karon daga cikin marubutan kansu, waɗanda ke ganin idan ba su motsa sun yi wannan gyaran ba to, wutar aka kunno don yaƙi da rubutun batsa, za ta iya kamawa har da su. Kamar yadda masu karatu da sharhi ke ta bambamin lalacewar rubutun adabi ba tare da warewa ba.

A yayin jawabin shugaban ƙungiyar GAMJIK wanda sakatariyarsa Rahama Usman Sabo ta wakilta, inda aka gabatar da taƙaitaccen tarihin ƙungiyar, marubuciya Rahama cikin kakkausan harshe da zubar da ƙwalla, tare da bayyana ɓacin rai da damuwar da marubutan adabi ke ciki, sakamakon yadda annobar rubutun batsa ke cigaba da ruruwa kamar wutar daji, kuma sakamakon haka ake ɗaukar akasarin sauran marubuta a matsayin waɗanda ke kauce hanya.

Ta bayyana cewa, duk hanyar da ta kamata su bi su ga sun jawo waɗancan baragurbin marubuta su tsarkake alƙalamin su, su dawo hanyar da aka san marubuta a kanta, ta gyaran tarbiyya, kawo sauyi a zamantakewar al’umma, faɗakarwa da nishaɗantar da masu karatu waɗanda suke wani vangare ne na al’umma.

Amma da dama daga cikinsu suka riƙa yin tutsu da haifar da rigima, cikin kalamai na ɓacin rai, da nuna isa da gadara, wanda ya tunzura wasu daga cikin marubutan da ke ganin wajibi ne a haɗa hannu a tashi tsaye a yaƙe su, tunda suna ganin ba a isa a dakatar da su ko a tauye musu ’yancin su na rubutu ba.

Malama Rahama Sabo ta bayyana aniyar ƙungiyar GAMJIK na haxa gwiwa da tsofaffin marubutan adabin Hausa, Ƙungiyar Marubutan Nijeriya ta ANA reshen Jihar Kano, Hukumar Hisba, Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano da sauran hukumomin da abin ya shafa, domin haɗa ƙarfi da samar da dokokin da za su ba da damar hukunta duk wani marubuci da ya kaucewa kyawawan tsari da manufofin da aka san marubuta a kansu.

Babu shakka wannan jawabi nata ya samu karɓuwa sosai a wajen ɗaukacin mahalarta taron, wanda ke nuna irin yadda wannan matsala ta daɗe tana ci wa marubuta tuwo a ƙwarya.

Kuma da alama a wannan karon a shirye suke su ba da dukkan haɗin kai da goyon bayan da ake buƙata, don kawo gyara da tsarkake harkar rubutun adabin Hausa da ta zama abin alfahari ga kowanne marubuci.

Shi ma a jawabin sa, Babban Baƙo Mai Jawabi, kuma ɗaya daga cikin magabatan marubuta, malami a Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Yusuf Adamu ya ƙalubalanci marubuta da su riƙa yin rubutun da tarihi zai tuna da su.

Sannan ya ce, a duk lokacin da marubuci zai rubuta labarin da ba zai iya karanta shi a gaban iyayen sa, ‘yan uwan sa ko ’ya’yansa ba to, babu shakka akwai abin ƙyama daga wannan rubutu da ya yi.

Duk irin rubutun da marubuci zai ji kunyar a danganta shi da shi a raye ko bayan ya bar duniya bai kamata ma bari ya shiga hannun jama’a ba, don ba a san iya hannun da zai shiga ba.

Bayan batun zubar da mutunci da kimar marubuta da ma’abota alƙalami ke kukan rubutun batsa yana jawo wa harkar adabi, marubuta musamman na yanar gizo ko kuma waɗanda ke sake rubutun su a giza-gizan sadarwa a ta bakin Farfesa Yusuf Adamu, suna.

Kuma qorafi kan yadda marubuta adabin bariki suka ƙwace kasuwar littattafan Hausa na zamani, saboda yadda masu karatu waɗanda akasarinsu matasa ne kuma mata, suka raja’a kan karanta irin waɗannan labarai da aka cika su da kalaman batsa.

Don haka sauran marubutan da ba sa bin waccan karkatacciyar hanya suka fara zama ‘yan kallo ko kuma a ce kasuwar su ta fara ja baya.

Wasu marubutan da suka rungumi wannan hanya ta adabin bariki da ba sa son a ambaci sunan su, na ganin ta inda baki ya karkata ta nan yawu ke zuba. In dai ana rubutu don riba ne da samun yawan mabiya da ke bibiyar littattafan da ake rubutawa to, dole a yi la’akari da abin da ya fi jan hankalin masu karatu, ta yadda duk saƙon da ake son isar wa zai iya samun shiga cikin hikima.

Wata daga cikin su na cewa, babu yadda rubutun labari da aka yi amfani da wasu kalamai na jan hankali zai zama dalilin lalacewar tarbiyyar wani ko wata, sai dai in dama can ba mai tarbiyyar ba ne.

Yayin da wannan muhawara ke ci gaba da ɗaukar zafi, shawarar mu a nan ita ce, hukumomi musamman na gwamnati, da malaman addini su shigo cikin wannan lamari, domin daƙile cigaba da ƙaruwar irin waɗannan rubuce-rubuce da ke tasiri a tsakanin matasa da matan aure, a samar da tsari na tacewa, da ƙa’idojin hana sa duk wani rubutu na batsa da ke karo da tarbiyyar addinin Musulunci da al’adun Hausawa, a kafafen sadarwa na yanar gizo.

Yayin da malamai za su cigaba da yin nasihohi da faɗakarwa kan illolin irin waɗannan rubuce-rubuce tare da ware gurɓatattu daga nagari.

Har wa yau, ina mai ƙara kira ga tsofaffin marubuta, maza da mata, da su shiga cikin wannan aikin alheri, a haɗa kai don kawo gyara da dawo da martabar rubutun adabi, da ƙara inganta yadda za a riƙa fitar da littattafan cikin tsari da kiyaye doka.

Sannan yana da muhimmanci bayan aikin gyare gyare da sa ido kan ayyukan adabi, gwamnati ta shiga cikin harkar ɗab’i da rubuce-rubuce, ta yi ruwa da tsaki tare da zuba jari, don ganin ta ci moriyar wannan ɓangare, da ya ke ɗaukar hankalin miliyoyin matasa, da samar da aiki ga ɗimbin masu cin abinci ƙarƙashin wannan harka ta rubutun adabi, ta hanyar shirya gasa kan wasu darussa na gyaran al’umma ko wasu manufofin gwamnati, yadda za a faɗakar da al’ummar ƙasa a kai, ta hanyar rubutu.

Sannan ƙungiyoyin marubuta da gwamnati su riqa shirya tarukan ƙara wa juna sani da bita ta hanyar haɗin gwiwa, don ƙara gogar da marubuta dabarun rubutu iri iri na zamani, inganta hanyoyin kasuwancin littattafai, da ƙarfafa gwiwarsu kan nazarin sauran ɓangarorin rayuwa da suka kamata a yi rubutu a kansu.

Allah ya ƙara haɗa kan marubuta, kuma ya ganar da waɗanda suka kuskure su ke rubutun da bai dace ba, don su daina, su zo a haɗa hannu a yi aiki tare, domin a gudu tare a tsira tare.