Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ƙara kasafin kuɗin zuwa miliyan 100 ga ɓangaren mace-macen mata masu haihuwa, domin inganta lafiyar mata da ƙananan yara.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Tsanyawa ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai a bikin ranar kula da lafiyar mata ta duniya da ake gudanarwa duk ranar 11 ga Afrilu, da aka yi a Litinin da ta gabata,
Kwamishina ya ce gwamnati ta ƙara kasafin ne domin amfanin mata da ƙananan yara daga miliyan 20 a 2015 zuwa Miliyan 100 a 2022.
“Gwamnatin jihar Kano ta horar da Mata 1,130 musamman akan lafiyar mata kuma muka tura su cikin yankunan danan-daban na jiha.
“Kuma mun maida hankali wajen ceto rayukan mata da ƙananan yara, inda muka bayar da horo ga ma’aikatan lafiya guda 220 domin ciyar da wannan fanni gaba” a cewarsa.
Taken bikin na bana dai shi ne “Samar da damar kula da lafiyar mata haƙƙi ne ga dukkan mata masu ciki.”
Ana bikin ranar ne domin wayar da kai kan kula da lafiyar mata masu ɗauke da juna biyu da kuma yayin haihuwar ƙananan yara.