Daga RABI’U SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta sanar da ɗage dokar hana fitowa da ta sa daga ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin da ta gabata.
Kwamishina Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Muhammad Garba ne ya sanar da haka a daren Lahadi nan data gabata zuwa safiyar Litinin.
Sanarwar ta ce duba da kwanciyar hankali da aka samu a faɗin jihar hakan ya bai wa gwamnati damar ɗage dokar ta awanni 24 da ta kafa don kare dukiya da rayukan al’ummar jihar
Kwamishinan ya buƙaci ‘yan kasuwar jihar da sauran masu gudanar harkokin yau da kullum haɗi da ma’aikatan bankuna da sauransu, da su fito su ci gaba da harkokin su kamar yadda suka saba.