Ganduje ya ƙi amincewa da buƙatar shugaban KARATO na neman yin murabus

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Muƙaddashin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, ya ƙi karɓar takardar ajiye aiki da shugaban Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) Baffa Babba Ɗan-agundi ya miƙa a ranar Litinin don yin murabus.

Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna Ɗan-agundi ya miƙa takardar ajiye aiki ga muƙaddashin gwamna don ba shi damar ajiye aikinsa amma sai Gwamnan Jihar, Umar Ganduje wanda ya tafi hutu can Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya bada umarnin kada muƙaddashin nasa ya karɓi takardar.

Sa’ilin da yake yi wa jaridar Solacebase ƙarin haske kan batun, Baffa Babba Ɗan-agundi ya tabbatar da ƙin amincewar da Gwamna Ganduje ya yi da yanƙurin ajiye aikinsa da ya yi.

Ɗan-agundi ya ce, ‘’Matsayin gwamna a gare ni ya zarce na shugaba, kamar uba yake a gare ni, don haka dole in karɓi abin da ya faɗa mini.

‘’Gwamna Ganduje shi ne wanda ya ɗora ni a kan matsayin Manajin Darakta wanda hakan ya bunƙasa mini rayuwata a siyasance.

”A gaskiya, ba zan iya saɓa wa duk abin da gwamnan ya yanke game da neman ajiye aikin nawa ba, saboda ya fi ni sanin abin ya da fi zama alheri a gare ni.”

Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa ya so ya ajiye aikin nasa, sai Baffa ya ce ya buƙaci hakan ne don cika burinsa na siyasa na neman tsayawa takara, amma yanzu dole ya dakata ya saurari abin da gwamna zai yanke.