Ganduje ya buƙaci Buhari ya ɗage ziyarar Kano saboda matsin da canjin kuɗi ya haifar

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar cewa ya aike wa Fadar Shugaban wasiƙar neman ɗage ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya kaiwa jihar.

Ganduje ya ce ya yi hakan ne saboda matsin da jihar ta faɗa sakamako wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira da CBN ya ƙayyade.

Ya ƙara da cewa, batu tsaro ma na daga cikin dalilan da suka sanya ya buqaci ɗage ziyarar ta Buhari zuwa jihar.

Gunduje ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawarsu tare da malamai da ‘yan majalisa da shugabannin siyasa da kuma ’yan kasuwar jihar a Fadar Gwamnatin Jihar.

Ya ƙara da cewa, an ɗauki wannan mataki ne domin kauce wa aukuwar abin da ba a shirya masa ba.

Da ma dai an shirya Shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki Jihar Kano domin ƙaddamar da wasu ayyukan cigaban da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *