Ganduje ya naɗa Khalid Musa hadiminsa kan sha’anin Kannywood

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya naɗa Khalid Musa a matsayin Babban Hadimi na Musamman (SSA) kan sha’anin masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, naɗin da ya soma aiki daga ranar 8 ga Fabrairun 2022.

Sanarwar naɗin na ƙushe ne cikin wasiƙar da sashen REPA da ke ƙarƙashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Kano, wadda Babbar Sakatariyar REPA, Bilkisu Shehu Maimota ta sanya wa hannu a madadin Sakataren Gwamnatin Jihar.

A cewar wasiƙar, an naɗa Musa a matsayin SSA ne duba da jajircewarsa, sadaukarwa a bakin aiki, sanin makamar aiki, ƙwazo da kuma biyayyar da yake da su, wanda ake fatan zai ci gaba da ɗabbaƙa waɗannan kyawawan ɗabi’u wajen gudanar da ayyukansa.

Gwamnatin Kano ta taya Khalid Musa murnar sabon naɗin nasa, tare da yi masa fatan gudanar da aikinsa babu kama hannun yaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *