Ganduje ya rufe kanti a Kano saboda ƙin karɓar tsoffin kuɗu

Daga HAMISU IBRAHIM a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da umarnin rufe katafaren kantin zamanin nan, wato Wellcare Supermarket, saboda ƙin karɓar tsoffin takardun Naira 200, 500 da kuma 1000.

Muƙaddashin Hukumar Kare Muradin Kwastoma na Jihar Kano, Dokta Baffa Babba Dan’Agundi ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan rufe kantin.

A cewar Dan’Agundi, aiwatar da umarnin na Gwamna ya zama wajibi sakamakon shagon ya ƙi karɓar tsoffin kuɗi wanda hakan ya saɓa wa umarnin Gwamna Ganduje da ya ce a ci gaba da amfani da tsoffin Naira a jihar.

Ya ƙara da cewa, za a ɗauki matakin shari’a a kan kantin, kana ya ja hankalin sauran ‘yan kasuwa a jihar kan su bi umarnin gwamnatin jihar sau da ƙafa sannan su ci gaba da amfani da tsoffin kuɗi.

Kodayake masu kantin, wato Wellcare Alliance Limited, sun aika da wasiƙar ban-haƙuri ga Gwamna Ganduje tare da neman ya sa baki a don a buɗe kantin ya ci gaba da aiki.