Ganduje ya yi wa fursunoni da dama afuwa

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ba da umarnin a saki wasu fursunoni 12 daga gidan yari a ranar Talata.

Wannan na zuwa ne yayi da ya rage kwanaki ƙalilaln kafin zaɓe gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a faɗin ƙasa.

Bayanin afuwar na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kakakin hukumar kula da gidan yari na Kano, SC Musbahu Lawan Ƙofar Nasarawa ya fitar ga manema labarai.

Sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya yafe ma waɗanda aka yanke wa hukuncin kisan ne a ranar Talata, kuma ya umarci a saki mutum shida da su ma aka yanke wa hukuncin kisa da aka sassauta musu zuwa ci gaba da rayuwa a gidan kaso wanda a yanzu suma sun shaƙi iskar yanci.

Kazalika, Musbahu Lawan ya ce haka wasu fursunoni mata su 4 da aka yanke ma hukuncin zaman kurkuku na tsawon lokaci, su na Ganduje ya bada umarnin a sake su sakamakon kyawawan ɗabi’un da aka shaide su.

Jami’in ya ce wasu daga cikin waɗanda aka ɗauren sun shafe shekara 25 suna jiran a zartar musu da hukuncin kisa.

Ɗaya daga cikin shugabanin da ke kula da ɓangaren yafiya na gidan yarin, Abdullahi Garba Rano, ya yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa afuwar da ya yi wa fursunonin bisa sahalewar doka.

Ganduje ya kuma raba ma waɗanda suka ci gajiyar afuwar Naira dubu biyar-biyar domin yin kuɗin mota zuwa gida.