Garaɓasar ranar Arfa

Wasu daga cikin yadda za ku tsara yin amfani da ranar Arafat kamar yadda ya da ce don cimma alfanu mai tarin yawa.

 1. Yin barci kaɗan a daren ranar Arafa.
 2. Tashi daga barci don yin salloli da sahur da niyyar ɗaukar azumin ranar Arafa.
 3. Sai yin sallar nafila raka’a biyu ko huɗu, sannan a tabbatar an yi adu’oi a yayin sujjada na samun duk alherin duniyar nan da na lahira, kar a manta a yi wa Allah godiya da Ya ba da ikon ganin wannan rana mai albarka wadda Allah (S.W.T) Ya ke bada alkhairai da yafiya ga al’umma ma su yawa.
 4. Kafin alfijir, ku kasance masu neman gafarar Ubangiji domin a lissafa ku cikin masu neman gafara da dare.
 5. Ku shirya yin sallar safiya sannan ku kasance ku ci gaba da neman gafarar ubangiji.
 6. Yi sallar safiyarku, bayan kammalawa, cigaba da zama a wurin sallan kuna masu karanta Al’kurani maigirma da yin zikiri.
 7. Yi sallar Shuruk bayan minti 15 da fitowar rana saboda ku samu ladar yin Hajji da Umrah kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya bayyana. Yi ƙoƙari kar wannan damar ta kubuce maku!
 8. Bayan sallar Shuruk, za ku iya yin barci don samun kuzarin yin azumin da ke bakinku.
 9. Za ku iya tashi ku yi sallar Dhuha (walaha) aƙalla raka’a huɗu sannan a ci gaba da yin zikiri da cewa; La’illaha Illal Lah Wahdahu La Sharika Lahu Lahul Mulku Wa Lahul Hamdu Wa Huwa Ala Kulli Shai’in Ƙadir.
 10. Yi sallar azahar, ku yi kabbara sannan ku karanta wani abu a cikin Alƙur’ani mai girma.
 11. Yi ƙoƙari ku saurari huɗubar Arafa a TV ko kuma a duk wata kafa da ta sauwaƙa.
 12. Yi sallar la’asar sannan ku cigaba da karatun Alƙur’ani da zikiri har magariba.
 13. Lokacin da magariba ta doso kamar awa ɗaya hakan nan, yi ƙoƙarin yin addu’oin neman gafara da albarkar Allah, sannan da duk wani alherin da ke cikin wannan duniya da lahira. Kar ku mance da sauran ‘yan uwa musulmai wajen addu’arku waɗanda su ke raye da matattu. Kar ku manta da ranar da za ku tsaya a gaban ubangijinku. Ku roƙi Allah Ya sa kuna daga cikin waɗanda za a gafarta wa kafin wannan ranar ta faɗi.
 14. Ku sha ruwa bayan sallar magariba, sannan ku kasance masu yin addu’o’i. Sai a yi, shi ke nan ranar Arafa ta ƙare!

Da fatan Allan Ya karɓi ayyukanmu na qwarai sannan Ya yi mana jagora, mu kasance masu yin ayyuka kyawawa, kuma da fatan za mu kasance a cikin bayinsa da Ya ke alfahari da su, Allah Ya kare ni da ku daga shiga wuta sannan Ya sa mu cikin waɗanda za a karci ayyukansu a ranar da ba abin da zai yi amfani sai ayyukan ƙwarai.

Daga Matashi mai kishin ƙasa, 09070905293.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *