Garkuwa: Kotu ta yanke wa Attajiri Evens ɗaurin rai-da-rai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babbar kotun Jihar Legas da ke Ikeja ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga wani hamshaƙin attajiri kuma ƙwararre a fannin garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike da aka fi sani da Evans da wasu mutane biyu, Uchenna Amadi da Okuchuwkwu Nwachukwu.

Mai shari’a Hakeem Oshodi ya yanke wa mutanen uku hukuncin ne a ranar Juma’a bayan da aka same su da laifuka biyu da suka haɗa da haɗa baki da kuma yin garkuwa da wani ɗan kasuwa, Donatus Duru.

Wanda lamarin ya rutsa da shi ya kasance Manajan Darakta ne na kamfanin Maydon Pharmaceuticals Ltd.

Da yake hukunta mutanen uku, Mai shari’a Oshodi ya ce, masu gabatar da ƙarar sun yi nasarar tabbatar da tuhumar da ake musu ba tare da wata shakka ba.

Da yake yanke hukunci a kan Evans, alƙalin ya ce, ya lura da halin da mai bayar da shaidar ya yi, inda ya bayyana cewa a wasu faifan bidiyo na ikirari da aka yi a kotu, Evans ya ambaci wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma da kuma rawar da suka taka a cikin laifin.

A ƙarshe ya ce, shaidun da suka gabatar a gaban kotu musamman furucin da suka yi na faifan bidiyon ya tabbatar da laifinsu.

Kotun ta sallami Ogechi Uchechukwu tare da wasu tsaffin sojoji biyu na sojojin Nijeriya Chilaka Ifeanyi da kuma Victor Aduba bisa rashin isassun shaidu da ke alaƙanta su da aikata laifin.

Gwamnatin Jihar Legas ta gurfanar da Evans a gaban kuliya tare da Uche Amadi, Okwuchukwu Nwachukwu, Ogechi Uchechukwu, Chilaka Ifeanyi, da kuma Victor Aduba bisa zarginsu da yin garkuwa da Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Maydon Pharmaceuticals Limited, Donatus Dunu, a ranar 14 ga Fabrairu, 2017.

Jihar ta yi ikirarin cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin ne tsakanin 14 ga Fabrairu zuwa 12 ga Afrilu, 2017.

Mai gabatar da ƙara ya ƙara shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:45 na dare, a kan titin Obokun, a unguwar Ilupeju a Legas.

Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotun cewa a ranar 12 ga watan Afrilu, Evans tare da sauran mutane biyar da ake tuhuma ɗauke da bindigogi da wasu makamai sun kama, sun tsare tare da karɓar kuɗin fansa na Euro 223,000 daga Donatus domin a sake shi.

Daga bisani gwamnatin Jihar Legas ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu a watan Agustan 2017.

Baki ɗaya, mai gabatar da ƙara ya gabatar da shaidu huɗu, ciki har da wanda lamarin ya rutsa da shi, Dunu yayin da mai kare ya gabatar da shaidu shida ciki har da Evans wanda ya bayar da shaida a kan nasa.

Haka kuma Evans yana fuskantar irin wannan tuhuma a gaban mai shari’a Oluwatoyin Taiwo da mai shari’a Adedayo Akintoye na kotun ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *