Garkuwar jikin ɗan’adam

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zaƙulo muku bayanai game da jikin ɗan’adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ke aiki.

Allah ta’ala Ya halicci duniya da abinda ke cikinta, Ya halicci jikin ɗan’adam wanda yake kewaye da abubuwan cutarwa iri-iri, na zahiri da na baɗini; amma cikin hikima da baiwa, da tausayi na Sarki mai tsara halitta, sai ya sanya wa ɗan adam garkuwar jiki domin ta zame masa kariya ga barin haɗari daga cutuka kala-kala.
Abubuwan da suke ba wa jikin ɗan’adam kariya sun haɗa da fata, fararen ƙwayoyin jini, da sauransu.

Yau idan sarkin ya so, za mu tunkari bayani game da garkuwar jikin ɗan adam gadan gadan, domin ilimintar da ku daga ɗan taƙaitaccen ilimin da na ke fama da shi. Saboda haka, ku biyo ni.
Kafin na nutsa, akwai buƙatar mu sani cewa, su ƙwayoyin halittar jini, musamman fararen, an yi su ne domin su taka muhimmiyar rawa wajen bawa jikinmu cikakkiyar garkuwar da ta dace. Duk da cewa wa’adin kwanakin da su ke yi a jikin dan adam taƙaitacce ne.

Haƙiƙa akwai wata babbar ƙwayar halittar (makrofej) mai haɗiye cututtuka, a turancin likita a na ce  ma ta “macrophage”. Babban aikinta shi ne haɗiye duk wasu baƙin halittu ko cututtuka irin su bakteriya da su ka shiga cikin jikin mutum.

Akwai kuma takwarar “makrofej” da ake kira da “neutrophil”, waɗanda su ma nau’i ne na fararen ƙwayoyin hallittar jini da su ke zubo da wani ruwan kemikal (wanda ƙarfinsa da kuma sigar aikinsa, kamar ruwam bilich yake: wato parazal ko kuma hypo). Wannan kemikal nasu na kashe ƙwayoyin cuta su ma. Sai dai akwai wani muhimmin banbanci tsakanin sigar aikin “makrofej” da kuma sigar aikin “nutrofil”.

Ƙwayar halittar makrofej, ta na bin ƙwayoyin cutar bakteriya ne ɗaya bayan ɗaya, ta na haɗiye su amma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci matuƙa; za ta iya ha]iye ƙwayoyin bakteriya sama da guda hamsin a duk sakwan ɗaya! A ɓangare guda kuwa, ƙwayar halittar nutrofil kamar bam take, mai ɗauke da sinadaran kemikal masu ƙarfin gaske. Da zarar ƙwayar nutrofil ta isa gurbin da baƙin halittu da cututtuka su ke, sai ta tarwatse, tare da lalata duk waɗannan abubuwa masu cutarwa, da ita kanta, a lokaci guda.
 
To bari mu ga wata ƙwayar halittar ta uku da ke ba wa jiki garkuwa ko kariya. Wanann ƙwayar halitta a na ce ma ta “natural killer cell”, (NK-cells a taƙaice) ma’ana “ƙwayar halitta mai ɗabi’ar kisa”. Ita ma nau’i ce ta farar ƙwayar halittar jini. Yadda take aiki shi ne—za ta samu bango ko katangar ƙawayar halittar da cuta ta harba, sai ta huda wannan bango ko katanga. Yin hudar ke da wuya sai ruwan jiki ya yi ta shiga cikin farfajiyar wannan ƙwayar halitta da ta kamu da cuta, haka shi zai jawo ta cika da ruwa ta kumbura daga bisani kuma sai ta fashe. Idan ta fashe, ta mutu kenan, jiki zai samar da wata ƙwayar halittar lafiyayya ta maye gurbinta.

Za mu iya cewa ƙwayar “natural killer cell” ‘oga’ ce, saboda aikinta na daban ne; ta na barwa makrofej da nutrofil ragamar kashewa da lanƙwame ƙwayoyin cuta. Amma kam duk ƙwayoyin halittar jiki da suka kamu a sanadiyyar shigar ƙwayar cuta cikin jiki, aikin “natural killer cell” ne kula da wannan ɓangare.

NK-cells suna da ƙarfi da tasirin gaske wajen fatattakar ƙwayoyin cutar bairos “virus” da suka kutsa cikin jikin ɗan adam; kuma suna ɗaya daga cikin tsayayyun dakaru  da jiki ke amfani da su wajen karya lagon cutar “cancer”, wato cutar daji.

Haƙiƙa waɗannan halittu na fararen jini suna iya banbance ‘yan gari daga baƙi. Ma’ana: su na iya bambance tsakanin ƙwayoyin halittun jiki daga ƙwayoyin cutar da su ka shigo cikin jiki. Yayin da waɗannan halittu da ke kare jiki su ka kaasa banbance tsakanin ‘yan gari’ da kuma ‘baƙi’, to fa matsala ta samu, domin za su dinga kaiwa ‘yan gida’, wato asalin ƙwayoyin halittun jiki farmaki, tare da lalata su. Wannan shi ke haifar da cutar da za mu iya kiranta da ‘kunar baƙin waken garkuwar jiki’, a turancinmu kuma “autoimmune disease”.

Yanzu bara mu ga ita garkuwar jiki. Idan a na magana a kan garkuwar jiki, akwai muhimman jiga-jigai guda biyu da dole sai anyi bayani akansu.  Dabbobi masu ƙashin baya (ciki hadda mutum, duk da cewa shi mutum ba dabba ba ne, amma an kasafta dashi cikin wannan aji na halittun Allah masu ƙashin baya), su na kuɓuta ne daga farmaki da hare-hare da su ke fuskanta daga ƙananan halittu masu cutarwa (microbes) saboda suna da garkuwa.

To domin kare kansu, sai Ubangiji Ta’ala ya sanya musu garkuwar domin ta tsaya mu su. Wato kamar dai yadda babban gari ko al}arya ke yi wajen tabbatar da tsaro da kula da kayayyaki da rayukan al’umma, haka shima jikin ɗan adam ke amfani da garkuwar jiki wajen karewa da kulawa da kuma tsarewa ga barin duk abubuwan da kan kawo naƙasu a lafiyar jiki. Kenan za mu iya cewa, jikin ɗan adam shi ma al’umma ce mai zaman kanta; al’umma ce ta ƙwayoyin halittu daban daban kamar ƙwayoyin halittar jini, da na fata, da na ƙwaƙwalwa, da na tsoka, da na ƙashi, da na ‘ya ‘yan rai na maniyyi, da na jijiyoyi, da sauransu.

Ga hanyoyin guda biyu: 
Na farko: akwai katangu masu tsayi da ƙarfi da ƙarko da ke kare manyan al’ummatai. Misalin wannan shi ne misalin badala da ta kewaye garuruwan ƙasashen Hausa. Waɗannan katangu na hana mayaƙa da ‘yan kai hari shiga cikin al’umma. To shima jikin ɗan adam na da wannan katangu masu bashi kariya. Babbar katangar da ke bashi kariya daga illar cututtuka masu yaƙi da jiki ta farko ita ce FATA.

Fata ita ce mataki na farko da ke wanzar da garkuwar jiki. Haka kuma, shimfiɗun tantanin dake kwance cikin sassa da gaɓɓan jiki masu hororo (mucous membranes) su na bada irin ta su garkuwar (domin sanin yadda fata ke bawa jiki kariya, ku jira rubutun da zanyi mai taken “Fata A Jikin ɗan’adam”).

Misalin, inda a ke samu waɗannan shimfi]u na tantani sun haɗa da: – hanyoyin iska ko numfashi (hanci, maƙogwaro, akwatun murya, bututun iska da rassansa) da kuma hanyar abinci (baki, bututun abinci (jannai), tumbi, ƙaramin hanji, uwar hanji, har zuwa dubura).

Na biyu: su ne jami’an tsaro masu kai-kawo. A jikin ɗan’adam, halittun da ke gudanar da wannan aiki suna amfani ne da ‘wutar chaji’ ko ince makamashin kuzari da su ke samu daga jiki, shi kuma jiki yana samun wannan makamashin kuzari daga abinci, da taimakon numfashi domin jiki yaci moriyar amfanin abincin. Bugu da ƙari, su waɗannan jami’ai su na samar da sinadarai na kemikal domin yaƙi da ‘yan kai hari da mayaƙa da ‘yan leƙen asirin jiki’ , kamar dai yadda ba ka rasa jami’an tsaro na zahiri da kayan aiki irinsu kulki, bindiga, ankwa, harsashi da sauransu; to su ma haka jami’an tsaro na jikin ɗan’adam su ke da tsari da shiri na fatattakar maƙiya. Kaji ikon Allah!

Kash! ‘Yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da yardar Sarkin Halitta, domin ci gaba da bayani a kan garkuwar jikin ɗan’adam.