Gasar Olympic ajin nakasassu ta Beijing tamkar madubi ne

Daga LUBABATU LEI

Nakassa ba kasawa ba ce, kamar yadda Bahaushe kan ce. A kwanan baya ne, aka rufe gasar Olympic ajin nakasassu ta shekarar 2022 ta Beijing, kuma a gasar ta tsawon kwanaki 9, ‘yan wasa nakasassu kusan 900 da suka fito daga ƙasashe da shiyyoyi 46 sun fafata a wajen gasar.

Abin lura a nan shi ne, a yayin gasar, ‘yan wasa nakasassu na ƙasar Sin sun yi nasarar lashe lambobin yabo da yawansu ya kai 61, ciki har da lambobin zinari 18, abin da ya sa ƙungiyar ‘yan wasan ƙasar Sin ta zo na farko ko a fannin yawan lambobin zinari da aka samu da ma ta yawan lambobin yabo da aka samu gaba ɗaya, sabanin yadda kungiyar ta lashe lambar zinari guda ɗaya kawai a gasar Olympic ta nakasassu ta Pyeongchang da ta gudana shekaru hudu da suka wuce, wadda ta kasance lambar zinari ta farko a tarihin ƙasar na halartar gasar.

Wannan saurin ci gaba da aka samu cikin shekaru huɗu kawai ba ma kawai nasara ce da ƙasar ta samu a fannin bunƙasuwar wasannin nakasassu ba, haka kuma ya shaida ci gaban ƙasar a fannin kare hakkin masu buƙata ta musamman.

Idan ba a manta ba, a gun bikin ƙaddamar da gasar a ranar 4 ga wata da ya gudana a babban filin wasan ƙasar Sin da ake kira “shekar tsuntsu”, gomman ‘yan wasa nakasassu sun “rera” taken ƙasar Sin ta hanyar yin amfani da alamomi masu lalurar rashin ji, wanda ya burge kowa da kowa. Baya ga fagen wasanni, ƙarin masu buƙata ta musamman na samun nasarori a fannonin rayuwarsu na yau da kullum, kamar yadda waɗanda ba su da wata nakassa suke yi, kuma hakan ba zai rasa nasaba da yadda ake ƙoƙarin kulawa da su masu buƙata ta musamman da ma kare haƙƙinsu a ƙasar Sin.

Akwai masu buƙata ta musamman kimanin miliyan 85 a ƙasar Sin, waɗanda yawancinsu suke fuskantar matsaloli ta fannin rayuwa da ma kulawa da su. Don haka, a shekarar 2016, ƙasar Sin ta kafa tsarin samar da kuɗin tallafi ga masu buƙata ta musamman da suke fuskantar matsalolin rayuwa da ma kuɗin kulawa da wadanda suke da nakassa mai tsanani. Daga shekarar 2016 zuwa 2020, tsarin ya shafi masu buƙata sama da miliyan 12 da suke fuskantar matsalolin rayuwa da ma wasu miliyan 14 da suke fama da tsananin nakassa. Daga shekarar 2021 zuwa 2025 kuma, tsarin zai game dukkanin masu buƙata ta musamman da ke fama da matsalolin rayuwa ko kuma tsananin nakassa.

Shugabar ƙungiyar masu buƙata ta musamman ta ƙasar Sin malama Zhang Haidi ta taba bayyana cewa, “Masu buƙata ta musamman suna iya kama sana’o’i iri iri kamar yadda waɗanda ba sa fama da wata nakassa suke yi.” Hakan abin yake, a nan ƙasar Sin masu bukata ta musamman suna da ‘yancin samun ilmi da guraben aiki kamar takwarorinsu waɗanda ba su da nakassa.

Alƙaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, daga shekarar 2016 zuwa ta 2020, gaba daya akwai masu buƙata ta musamman da suka ci jarrabawar shiga jami’o’i, ƙaruwar kaso 50.11% kwatankwacin na shekarar 2011 zuwa ta 2015, baya ga kuma wasu ƙarin miliyan 1.81 da suka samu guraben aikin yi a cikin garuruwa. Ban da haka, masu bukata ta musamman kimanin dubu 400 ne su kan samu damar shiga kwasa-kwasai na horar da fasahohin sana’o’i da gwamnatin ƙasar ta ɗauki nauyi.

A gasar Olympic ajin nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing, yadda aka samar da wani yanayi na kawar da matsaloli ga dukkan ‘yan wasa nakasassu na kasashe daban daban ya burge kowa, kuma hakan wani ɓangare ne na yadda ƙasar Sin ke kokarin kawar da matsaloli ga masu buƙata na musamman a ƙasar, inda aka gyara kimanin kashi 38% na ban daki dake kauyuka da unguwannin ƙasar, don masu bukata ta musamman su samu saukin yin amfani da su. Baya ga haka, an kuma gyara jiragen ƙasa da motocin bas don saukaka musu……

Yadda aka samar da tabbaci da ma dada kyautata rayuwarsu ya zama tushen yadda masu buƙata na musamman na ƙasar Sin ke ƙoƙarin shiga harkokin wasanni da ma sauran fannonin zamantakewar al’umma. Gasar Olympic ajin nakasassu ta Beijing tamkar madubi ne, wadda ta shaida ci gaban harkokin wasanni na masu buƙata ta musamman, da ma ingantuwar yanayin da suke ciki.

Kamar yadda mataimakin shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na lokacin hunturu na Beijing, Mr.Yang Shu’an ya fada, “sakamakon ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma, an kara kulawa da nuna goyon baya ga harkokin wasanni na masu buƙata ta musamman, tare kuma da yadda su kansu suke ƙoƙarin, duk wadannan su ne suka taimaka mana wajen samun nasarar.”