Gasar Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing ta nuna nasarar da Sin ta cimma a fannin kare haƙƙin ɗan Adam

Daga CRI HAUSA

A daren yau ne, za a buɗe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing a hukumance, inda yan wasan motsa jiki daga ƙasashen duniya za su yi ƙoƙarin samun nasara a wannan dandali mai muhimmanci.

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na ƙasa da ƙasa Andrew Parsons ya ce, masu aikin sa kai na birnin Beijing suna da himma da kwazo, yadda suke gudanar da ayyukansu, ya nuna min yadda alummar Sin suke karɓar baƙi da hannu bibbiyu.

Ƙasar Sin ta duƙufa wajen shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu bisa Ƙa’idojin kare muhalli, yin haɗin gwiwa, bude kofa ga waje, da kuma yaki da cin hanci da karɓar rashawa, ta yadda za a tallafa wa ‘yan wasannin motsa jiki na nakasassu kamar yadda suke buƙata.

Haka kuma, za a ci gaba da amfani da naurorin da aka yi amfani da su a gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, da kuma gyara su domin dacewa da buƙatun nakasassu.

Gwamnatin Ƙasar Sin ta kuma fidda takardar bayani mai taken wasannin masu buƙatar musamman, inda aka yi cikakken bayani kan yadda aka raya wasannin motsa jiki tsakanin rukunin mutane masu buƙata ta musamman, da kuma taimaka musu cimma burikansu.

Ana sa ran cewa, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu da za a yi a birnin Beijing, za ta ƙara ƙwarin gwiwa tsakanin rukunin mutane masu buƙata ta musamman, da ƙara fahimtar da gamayyar ƙasa da ƙasa game da bukatun mutane masu buƙata ta musamman.

Fassarawa: Maryam Yang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *