Gasar Zakarun Turai: Arsenal da Barcelona sun kai zagayen kusa da ƙarshe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Arsenal ta kai zagayen daf da na kusa da na ƙarshe, bayan da ta yi nasara a kan FC Porto da cin 4-2 a bugun fenariti ranar Talata a Emirates.

Tun farko Arsenal ce ta ci 1-0 ta hannun Leandro Trossard saura minti hutu su je hutu, irin wannan sakamakon Porto ta samu a Portugal a wasan farko.

Hakan ne ya sa aka yi ƙarin lokaci daga nan aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Gunners ta ci ƙwallaye a bugun fenariri ta hannun Odegaard da Kai Havertz da Bukayo Saka da kuma Declan Rice.

Mai tsaron ragar Arsenal, David Raya ya tare kwallon da Wendell da na Galeno da suka buga masa.

Da wannan sakamakon Gunners ta kai kwata fainals a Champions League a karon farko tun 2009/10.

Haka kuma Gunners ta kawo ƙarshen rashin nasara bakwai a jere a zagayen ‘yan 16 a gasar ta zakarun Turai.

Leandro Trossard ya zama na uku da ya ci kwallo a wasa uku a Champions League a gidan Arsenal, bayan Alexis Sanchez da kuma Bukayo Saka.

Martin Odegaard ya bayar da ƙwallo bakwai aka zura a raga a bana a dukkan fafatawa har da ɗaya a gasar Zakarun Turai.

Mai tsaron bayan Porto, Pepe ya zama na farko da ya buga gasar zakarun Turai yana da shekara 41.

Haka zalika, Barcelona ta kai zagayen kusa da ƙarshe a gasar Zakarun Turai, bayan da ta doke Napoli 3-1 a Sifaniya ranar Talata.

Barcelona ta kai zagayen gaba da cin ƙwallo 4-2 kenan gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 a wasan farko a Italiya.

Barcelona ta kai zagayen daf da na kusa da na ƙarshe a gasar zakarun Turai a karon farko tun bayan 2019/20.

A kuma lokacin ƙungiyar Sifaniya ta yi nasara da cin ƙwallo 4-2 gida da waje a kan Napoli.

An yi waje da Napoli a Champions League a irin wannan mataki karo huɗu daga fafatawa biyar – haka kuma ƙungiyar Italiya ta yi rashin nasara a wasa biyar daga shida a zagayen zuri ɗaya tal.