Gaskiyar magana game da rashin samun miji ko matar aure

Daga AMINA YUSUF ALI

Wannan maudu’i da za mu tattauna wannan mako, za mu duba yadda ake yawaitar samun samari da ‘yammata/zarawa marasa aure a garin nan. Ƙasashen Hausa cike suke da waɗannan matsaloli. Kuma kowa ka taɓa cikin waɗannan matasan sai ya ce ai ya rasa miji ko matar aure ne. Wasu lokutan ma har a kafafen sadarwa ko dandalin sada zumunta na yanar gizo daban-daban za ka ga an ba da cigiyar mutum yana neman matar aure iri kaza, ko mai kama kaza. Haka su ma matan sukan ɓoye sunansu na ainahi su tallata kansu a waɗancan kafafen don a samo musu irin mazajen da suke buƙata. A yanzu haka zaurukan ƙulla ala}ar aure sun yawaita sosai a shafukan yanar gizo. Amma daga ina matsalar take? Domin yadda maza suke kokawa da rashin samun mace haka mata ke yi. Amma abin mamakin sai a ga mata/maza birjik a danginsu, ko a wajen aiki/sana’a, ko a unguwarsu da sauransu.

Abu na biyu kuma shi ne, sai ka ga namiji yana da ‘yammata birjik, amma duk da haka kullum fafutukar neman matar da zai aura yake yi. Haka mace ma wata za ka same ta da tarin samari birjik, amma ita ma kana taɓa ta za ta ce ai ba ta samu mijin aure ba. To wai ina matsalar take ne? Kada fa mu zama abinda wata karin maganar Hausa take cewa: ‘Da magani a gonar yaro…’ Wato mutum yana tare da maganin matsalarsa amma bai gano ba. A nazarin da na yi, na gano cewa, ba wai abokin rayuwa ake rasawa ba, illa dai kawai rashin samun daidaito. Ga wasu nazari da na yi a kan haka:

  • Rashin samun abokin rayuwar da ya dace: Wato za ka ga mace da tarin samari birjik amma kuma ba wanda ya kwanta mata a rai. Wato ba wanda ta ji tana yi masa irin son da za ta iya ƙarashe rayuwarta tare da shi. Haka shi ma namijin. Wasu sun ce ma daga zarar ka haɗu da irin wannan matar ko mijin za ka ji a jikinka wannan shi ne wanda kake burin haɗuwa da shi ɗin. Shi ya sa sai ka ga saurayi yana tsallakawa daga wannan yarinya zuwa waccan amma bai ji wacce ta kwanta masa a rai har da zai sakankance da ita ta zama abokiyar rayuwarsa ta din-din-din ba.
  • Rashin dacewa/saɓawar halayyar juna: Kamar yadda na faɗa a sama, so yana matuƙar tasiri wajen ƙulla alaƙar da za ta kai ga aure. Amma duk da haka, sai halayya ta daidaita ko ta saɓa. Wasu masoyan sukan iya fara soyayya kan jiki kan ƙarfi, amma sai rashin fahimtar juna ya sa a yi ta ɓatawa. Ƙarshe dai a zo a rabu. Idan halayya ta zama ɗaya kamar an samu mara haƙuri da takwararsa mara haƙuri, sai a yi ta saɓawa. Daga ƙarshe a rabu. Yawan faruwar haka zai sa a yi ta canza sheƙa. Har ma daga ƙarshe mutum ya ba da cigiya don samun matar da yake so. Kwaɗayi: Akwai matan da suna aamun manema sosai. Amma masu ƙaramin ƙarfi ne ko tsaka-tsaki. Waɗanda take ganin ba tsararrakinta ba ne a aure. Kuma waɗanda take buri su zo su aure ta kuma ba su samu ba. Wasu ma har da ƙarya sukan zo mata amma daga ƙarshe idan bincike ya zurfafa, sai a ga ashe dai basaja ya yi mata. Irin wannan buri yana zaunar da mata da yawa a gidan iyayensu. Wasu daga ƙarshe burinsu ya cika, wasu kuma burikansu ba sa cika. Daga ƙarshe sai ta haƙura ta auri wanda ya samu. Ko kuma idan aka yi rashin sa’a ta samu maƙaryaci wanda ya ƙware a ƙaryar arziki. Haka za ta ɗauki kara da kiyashi da hannunta. Kazalika shi ma namiji mai burin auren mace mai maiƙo yakan daɗe a ƙasa bai samu shiga ba. Wani zai ta hanƙoron ‘yar mai kuɗi ko wata attajirar bazawara ko wacce aka mutu aka bar mata Dukiya. Amma sai ka ga shi a tsarin halitta da halayyarsa kwata-kwata ba ta iya jan ra’ayin waɗancan mata da yake ta hanƙoro. Sai ka ga yana ta lalube don cikar burinsa. Idan bai samu ba sai ka ga ya baza komarsa a wajen masu dalili na zahiri da na zaurukan yanar gizo ko za a dace. Fasalin mace ko namijin da ake so: kamar yadda Bahaushe yake cewa, wai shan koko ɗaukar rai, ra’ayin mutum yana tasiri matuƙa wajen zaɓar abokin rayuwar aure. Kowanne ɗan-adam, walau mace ko namiji yana da ra’ayinsa game da wanda ko wacce zai aura. Sai ƙalilan waɗanda suke duba halayyar wanda za su aura. Su ajiye ra’ayin nasu a gefe. wasu matan sun fi son kyakkyawan namiji ko su ce dogo, wasu su ce sun fi son mai saje, wasu kuma su ce fari ko baƙi da sauransu. Hakan su ma mazan sukan ce sun fi son fara, ko baƙa, ko mai tsawo, ko gajera, ko siririya, ko mai ƙiba, da sauransu. Amma inda matar ke ka da mijin shi ne, ita wacce kake son kai ka yi mata? Ko ke wanda kike ra’ayin ina za ki samo shi? Shi ya sa sai a yi ta lalube wani a dace a kusa, wani a samu jinkiri sannan a dace, wani ma kuma sai dai a haƙura da abinda ya samu. Sanayya tana kawo raini: Wasu kuma suna ƙin auren na kusa da su kamar a dangi ko maƙwabta ko abokan aiki saboda gudun kada a raina su. Wato suna ganin wanda ya san asalinka har ma ya san wasu abubuwa masu kyau da marasa kyau da suka faru da rayuwarka ko zuriyyarku to zai iya goranta maka ko miki nan gaba a rayuwa. Ko kuma kai ɗin ko ke ɗin kun taɓa aikata wani abu na Allah wadai a rayuwarka/ki wanda makusantanku suke tsoron haɗa nasaba da ku. Duk da dai kamata ya yi a dinga uzuri ga wanda ya tuba da aikata wani laifi. Rashin sana’a ga maza: Su kuma maza wani lokacin ga ‘yammatan sun samu a hannu. Amma rashin sana’ar da za su ha]a kayan auren sun zama cikas a wajensu. Ko da ya fara neman yarinya idan aka nemi ya fito ya ƙi, za a ɗauke shi mayaudari kuma a dakatar da shi. Idan kuma aka samu wanda yake da sana’a ya fito yana sonta, sai ka ga an ajiye shi gefe an ba da yarinyar ga wanda yake da sana’a. A nemi sana’a maza! Cimma buri: Wasu mazan ko matan suna son su yi auren amma akwai wasu burika da suke son cimmawa kafin au yi aure. Akwai darussa da yawa a makaranta waɗanda ba a haɗa su da aure. Irin wannn yana sa a yi ta ganin mace kamar tana korar samari. Amma ni a ra’ayina aure ba ya hana ilimi. Kamata ya yi ta yi aurenta kuma ta ci gaba da karatunta. Rashin samun na kirki: Samari da ‘yammata da dama sukan fa]a ƙaddarar rashin dace. Inda za a ga saurayi ya samu budurwa rumi-rumi, sai tafiya ta yi tafiya a gano ba mutumin kirki ba ne. Wani ma wata manufar ta kawo shi ba auren ba. Daga ya cim ma manufarsa, sai ya ƙara gaba. Idan kuma ya ha]u da yarinyar kirki sai ta kore shi. Wasu matan suna jin kunyar bayyana wa iyayensu cewa ga abinda ya wakana tsakaninsu da manemansu. Sai kuma ka ga ana zarginta da korar samari. Lokaci: Wasu kuma suna samun samarin sosai ko ka ga an ja dogon lokaci ana soyayya amma ba a yi aure ba. Wani lokacin auren ne kawai bai yi ba. Daga lokaci ya yi ba makawa za a ga an yi komai an wuce wajen. Ruwan ido: A gaskiya wasu samarin da ‘yammata suna da ruwan ido da tsananin tsirfa wajen zaɓen abokin rayuwa. Sai ka ga ‘yar tawaya kaɗan, ta sa sun fasa auren wani ko wata. Kowa gani suke bai yi musu yadda suke so ba. Kasancewar ɗan-adam babu kammalalle marar tawaya, shi ya sa masu wannan ra’ayi suke shan wahala wajen zaɓen abokin rayuwa. Amma da za su gano cewa su kansu suna da tawaya irin wacce suke hangowa a jikin waɗanda suke fasa aura ]in, da sun huta wa zukatansu. Shafar aljanu/Sihiri: Kamar yadda muka sani, shaiɗanu suna da matuƙar adawa da aure kuma duk wata hanya da za su bi su ga an wargaza shirin sun hana aure ƙulluwa, suna yi. Haka akwai shaiɗanun mutane waɗanda kan jefi wata mace ko namiji su hana shi aure. Sai an shirya magana sai ta wargaje. Don haka idan irin wannan matsalar tana yawan faruwa, sai a nemi maganin shafar aljanu da na sihri. Don wani in dai ba a yi ba, sai dai su zauna har abada ba aure.

Daga ƙarshe, ya kamata mutane su sani, faɗar wane ya ƙi aure ko wance ta ƙi aure tamkar fami kake yi wa zuciyarsu. Kowa yana son ya yi auren nan sai dai idan ɗaya daga cikin dalilan nan ne ya gifta. Bissalam. Sai mun sake haɗuwa wani makon.