Gawuna ya taya Abba Kabir murnar lashe zaɓen Gwamnan Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna a jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya taya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, murna.

Ta cikin wani sako na murya da mai magana da yawunsa, Hassan Musa Fagge, ya saki a manhajar WhatsApp a ranar Laraba, Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida addu’ar Allah Ya sa ya zama shugaba nagari.

A cewar Gawuna, tun bayan da hukumar zaɓe, INEC, ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen, jam’iyyar APC ta rubuta ƙorafe-ƙorafe kan cewa a duba sakamakon zaɓen da kyau domin akwai kura-kurai.

Ya ƙara da cewa, duk da wannan yunƙuri da APC ta yi na a sake tantance sakamakon zaɓen tare da sake zaɓuka a wasu gurare, amma INEC ɗin ta miƙa wa Abba shaidar lashe zaɓe.

“Saboda haka, tun da hukumar zaɓe ta daɗa tabbatarwa da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen a yau, 29 ga watan Maris, to ina mai tuna wa magoya bayanmu cewa tun a baya mun yi addu’a cewa in alheri ne, Allah Ya ba mu, in kuma babu alheri, Allah Ya canja mana da abin da ya fi alheri.

“Shi kuma wanda ya ci zaɓen, muna masa addu’ar Allah Ya sa ya zama shugaba nagari.

“Muna yi wa magoya bayanmu godiya bisa fitowa da suka yi mazansu da matansu suka zaɓe mu. Kuma ina kira ga magoya baya da mu zamana masu yarda da ƙaddara.

“Mu ma addu’a Allah Ya sa mu zama masu biyayya ga shugabanci da kuma bin doka. Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya,” in ji Gawuna.