Gawurtaccen ɗan fashin daji, Dogo Gide ya cimma ajalinsa a kurmin Kuyanbana

Daga BASHIR ISAH

Bayanai daga jihar Kaduna sun tabbatar da cewa, gawurtaccen jagoran ‘yan fashin dajin nan, wato Dogo Gide, ya sheƙa lahira biyo bayan saɓanin da ya shiga tsakaninsa da na ƙasa da shi.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa, Dogo Gide ya cimma ajalinsa ne a kurmin Kuyanbana da ke jihar Kaduna a Lahadin da ta gabata.


Idan dai za a iya tunawa, a watan Maris na 2018 Gide ya kashe ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan mai suna Buharin Daji, inda ya zama mai mulkin gandun nasu.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa PRNigeria cewa mataimakin gungun Gide mai suna Sani Ɗan Makama, shi ne halaka Gide saboda rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu.

Kafin wannan lokaci, Gide ya addabi wurare da dama da ta’addancinsa da suka haɗa da wasu ƙauyukan jihar Zamfara da Neja da Kaduna da Katsina da kuma Kebbi na tsawon shekaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *