Gazawa ce idan APC ta jajubo Jonathan a 2023 – Hon. Tasiu Danhajiya

Daga NASIR S. GWANGWAZO

An bayyana cewa, ba ƙaramar gazawa ba ce ga jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya matuƙar ta yi kuskuren bai wa tsohon Shugaban Nijeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, takara a lokacin Babban Zaɓen shekara ta 2023 da ke tafe.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Hon. Tasiu Sani Danhajiya, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano da Kewaye kuma ɗan jam’iyyar APC.

Idan dai za a iya tunawa, rahotanni na nuni da cewa, akwai wani tsari a ƙarƙashin ƙasa da ake yi tsakanin wasu jiga-jigan APC daga Arewacin Nijeriya na dawowar Mista Jonathan cikin APC, domin tsayar da shi takara a Babban Zaɓen 2023 bisa dogaro da cewa, zango ɗaya ne kawai ya rage ma sa na mulki na shekara huɗu maimakon zango biyu, wato shekara takwas, inda idan ya kammala zai dawo da mulki ga Arewa a 2027 saɓanin 2031, idan da shekara takwas ya ke da ita.

To, amma sai dai daga dukkan alamu wannan tsari bai yi wa wasu ’yan jam’iyyar daɗi ba, inda Hon. Danhajiya na daga cikin masu wannan ra’ayi na suka ga jajubo Jonathan.

A tattaunwarsa da Manhaja, Danhajiya ya ce, “wasu za su yi fushi, wasu za a ɓata musu da yawa, domin Jonathan ɗin nan a hannunsa aka karɓi mulkin nan a na ta cewa bai iya ba, ya gaza, mu ma muka zo mu ka karɓa! To, kuma yanzu idan a na so a mayar ma sa, to me ake nufi kenan? Ana nufin to shi ya fi mu ma iyawa kenan?

“To, wannan shi ne kawai tunaninmu, mu matasan jam’iyya. Amma da kawai zai shigo jam’iyya ne ya taya a ci gaba da raya ta, to shikenan idan wani lokacin ya yi, idan ya na da wani rabon, sai ya samu. Amma a ce kawai ya zo a ba shi takara, gaskiya ba zai yi wa da yawa daɗi ba!”

Tasiu Danhajiya ya kuma ƙara da cewa, “ana ta raɗe-raɗin Jonathan zai dawo APC, don ana so a ba shi takara a 2023. Ni abin da ya ke damu na a jam’iyyar nan shine, yaya za a yi alƙawuran da muka yi wa jama’a a isar da shi kafin wannan lokaci na cewa takara ta zo!

“Mai girma Shugaban Ƙasa yana iyaka ƙoƙoraninsa. To, dole a duba a ga wane ne zai zo ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari. To, a tunani shine wasu suke ƙoƙarin ya za a yi Jonathan ya dawo, don a ba shi takara a Jam’iyyar APC?”

Ya ci gaba da cewa, “Magana ta Allah tun da ya yi Shugaban Ƙasar nan kuma yana da ragowar zango guda ɗaya, meye amfaninsa idan ya dawo APC, idan ba takara zai yi ba? Ka ga jam’iyyar nan ita ta ke da rinjaye a gwamnoni da ’yan majalisar tarayya da sanatoci. To, meye amfanin Jonathan idan kawai dawowa zai yi APC, don ya raya ta? Ai a raye ta ke! Amma a tunanina matuƙar ɗin ya dawo, takara ya ke son yi ko ake son a ba shi.”

Sai kuma ya yi hannunka mai sanda da cewa, “idan abin ya fi ƙarfinka ya za ka yi? Amma dai magana ta Allah, mu idan a son sonmu ne, za mu fi so a ɗauko wani a ba shi takarar nan a jam’iyyarmu, ba wai wani wanda ya shigo ba. Gara a bai wa ’yan asalin jam’iyya, waɗanda aka je Zamfara aka ƙaddamar da ita da su, suaka wahala a jam’iyyar nan, ake faɗi-tashi da su.

“Amma magana ta Allah a ce wai wani ya zo an ɗauki takara an ba shi, to Ina jin duk mutanensa na can baya da su zai yi harka, ba da namu ba, domin su ya sani. To, ka ga kuma za a yi baɗi ba rai kenan, domin ka ga akwai mutanenmu da suka wahala, amma har yanzu ma su na ganin an yi tafiyar nan, amma har yanzu ba su amfana ba.”

Idan dai za a iya tunawa, Shugaban Ƙasa mai ci, Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC sun amshi mulki a hannun Jonathan ƙarƙashin tutar Jam’iyyar PDP ne a 2015 bayan da suka kayar da shugaba mai ci, wato Shugaba Jonathan, a wancan lokaci.