Gbajabiamila na shirin zama shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a gwamnatin Tinubu

Daga WAKILINMU

Alamu sun nuna Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, na shirin zama shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ga zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, a gwamnati mai zuwa.

Bayanai sun ce hakan ba ya rasa nasaba da ƙin zuwa karɓar shaidar lashe zaɓe da Gbajabiamila ɗin ya yi inda INEC ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga ‘yan Majalisar Wakilai da suka kai bantensu a ranar Larabar da ta gabata a Abuja.

An sake zaɓar Gbajabiamila don wakilcin yankin Surulere 1 a Jihar Legas, wanda wannan ya zama karo na shida da yake lashe zaɓe a shiyyar.

Sai dai majiyarmu ta ce mai yiwuwa ba zai wakilci shiyyar nasu ba a Majalisar ta Wakilai wannan karon, saboda ‘yar manuniya ta nuna akwai yiwuwar a naɗa shi shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa na zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a sabuwar gwamnati mai zuwa.

Majiya ta kusa da Gbajabiamila ta bayyana cewa, kasancewarsa ɗaya daga cikin ‘yan ga-ni-kashenin Tinubu kuma a wanda aka dama da shi a harkokin siyasa shekara 20 da suka shuɗe, akwai yiwuwar Gbajabiamila ya samu wannan matsayi.

Game da makomar zaɓen da Gbajabiamila ya lashe, ko zai bar majalisar ya tafi neman muƙami a gwamnatin Tinubu ne?

“Abin da muke ji kenan. Idan aka lura bai je ya karɓi shaidar lashe zaɓen da ya yi ba wanda aka raba wa takwarorinsa ranar Laraba. Gaskiyar ita ce, ba ya da buƙatar shaidar.

“Yana da ƙwarewa da cancantar riƙe matsayin shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a sabuwar gwamnati mai zuwa. Ya yi aiki da ‘yan siyasa da damaa tsakanin shekaru 20 da suka gabata,” in ji majiyar.