Gbajabiamila ya sake taɓa zukatun jama’a a mazaɓarsa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Kakakin Majalisar Dokoki ta Tarayya, Femi Gbajabiamila, a ranar Asabar da ta gabata ne ya kuma rarraba tallafi wa jama’ar mazaɓar sa ta Surulere 1 da ke birnin Ikko, inda ɗimbin mutane suka amfana.

A wani ƙasaitaccen shiri na miƙa hannu wa jama’ar mazaɓar sa, wanda aka gudanar a filin wasa na Teslim Balogun dake birnin Ikko, an bayar da tallafin ƙaro ilimi wa ɗalibai 351dake jami’o’in gwamnati da a halin yanzu suke karatu a sassa daban-daban na ƙasar nan, yayin da shugabannin makarantun sakandare guda 1,020 aka ba su na’urorin kwmfuta domin su sauƙaƙa masu wasu matsalolin koyarwa.

Bugu da ƙari, an raba motoci guda 145, waɗanda suka haɗa da motocin ɗaukar gawa da majinyata, motocin jami’an tsaro da na’urorin inganta lamuran tsaro, haɗi da motoci bus-bus ga ɗalibai a makarantu.

Bikin raba kayayyakin tallafin, wanda ya samu halarcin shugaban jam’iyyar APC na jihar Ikko, Honorabul Cornelius Ojelabi, da tsohon mataimakin gwamna na jihar ta Ikko, Femi Pedro, tsohon minista Sanata Musiliu Obanikoro, haɗi da wasu jami’an gudanar da mulki, inda aka kuma rarraba tallafin kuɗaɗe wa masu matsakaitan masana’antu guda 1,596 mazauna mazaɓar ta Surulere 1.

Wannan rarraba kayayyakin tallafi da kuɗaɗe dai ya biyo bayan ƙaddamar da cibiyoyin fasahar kimiyya (ICT) da ɗimbin makarantu da aka yi wa kwaskwarima ne a mazaɓar ta Surulere da Femi Gbajabiamila ya gudanar.

Da yake yin jawabi a wajen bikin, Gbajabiamila ya ce an shirya taron ne domin nuna godiya da inganta mu’amala a tsakanin ɗan majalisar ta ƙasa da jama’ar mazaɓun sa.

“Wajibi ne a garemu a matsayin mu na ‘yan majalisa mu kyautata wa jama’ar mazaɓun mu domin cimma biyan buƙatun su na yau da kullum. A kullum ina da sha’awar bunƙasa lamuran ilimi, don haka nake tayin ƙoƙarin ganin na cimma biyan bukatun ɗalibai da malamai dake wannan mazaɓa ta Surulere 1.

“Wannan ya biyo bayan ayyukan gine-gine da muka samar wa wannan mazaɓa da makwabtan ta. Daga gina hanyoyi zuwa sabbin asibitoci, daga gina cibiyoyin fasaha a matattarar jama’a zuwa samar wa matasa aiyukan yi, haɗi da samar da muƙaman siyasa domin samun wakilci nagari a gwamnati.”

Ya ƙara da cewar, “mun kuma ci nasarar samar da wutar lantarki wa dukkan hanyoyi dake cikin mazaɓar mu ta Surulere, da ya bunƙasa tattalin arziki, tsaro da zama lafiyar jama’ar mu. Muna kuma ta yin kazar-kazar domin samun ƙarin ayyukan cigaba. Dangane da lamuran wassanni kuwa, mun gina matsakaitan filayen wassanni a sassa daban-daban na mazaɓar mu ”

Kakakin majalisa sai ya yaba wa ɗaya daga cikin jama’ar mazaɓar ta Surulere, Mr Saheed Okunu wanda ya amfana da motar ɗaukar dako a tallafi daya bayar na shekara ta 2020, “kuma yayi amfani da tallafin wajen inganta rayuwar sa, ya kuma sayo wata makamanciyar motar, kuma ina nuni da shi wajen yin misali gareku, musamman ga waɗanda suke da miyyar sayen motoci daga cikin ku”, ya ƙara da cewar, za’a sake ƙarfafa wa Mista Okunu da ba shi wata motar domin bunƙasa kasuwancin sa.

“Motocin safara sun kasance sun kasance jigo na bunƙasa tattalin arzikin jama’a a dukkan sassa na duniya, har da ƙasar Nijeriya, ta kasance kusan gidan kowa da akwai, dake bunƙasa tattalin arziki,” inji Gbajabiamila.

Ya yi matuƙar farin ciki da cewar, kusan dukkan malaman makarantun sakandare dake mazaɓar Surulere sun amfana daga na’urorin fasaha na bunƙasa koyarwa a makarantu.
“Addu’a ta ita ce waɗannan tallafi ya taimaka matuƙa gaya wajen inganta rayuwar jama’a, da buɗe masu rayuwa ta gari a nan gaba.

“Zan kuma ci gaba da sadaukar da kai na wajen tabbatar da wanzuwar dokoki da za su inganta rayuwar jama’a, haɗi da ƙarin tallafe-tallafe waɗanda za su bunƙasa rayuwa da ci gaban jama’ar mu, haɗi da samar da turakun ci gaba, samar da ayyukan yi, da tallafi wa jama’a.”

Kakakin majalisar dai ya samu kyawawan yabo daga ɗaukacin mahalar ta bikin raba tallafin, waɗanda suka jinjina masa bisa abubuwan alheri da nagargaru da yake yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *