GDPn watannin 6 na farko na bana na Ƙasar Sin ya ƙaru da kashi 2.5

Daga CMG HAUSA

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa na ƙasar Sin, ya kira taron manema labarai yau da safe, don bayyana yadda ake tafiyar da tattalin arzikin ƙasar Sin a farkon watanni 6 na bana.

Alƙaluma na nuna cewa, GDPn ƙasar a watanni 6 na farkon bana, ya kai kuɗin Sin Yuan biliyan 56264.2, wanda ya karu da kashi 2.5% bisa na makamancin lokaci na bara. Daga cikinsu, sha’anin gona da na masana’antu da ba da hidimma, sun samu karuwar da ta kai Yuan biliyan 2913.7 da Yuan biliyan 22863.6 da Yuan biliyan 30486.8. Wanda ya ƙaru da kashi 5.0% da kashi 3.2% da 1.8% bisa na makamancin lokaci na bara bi da bi.

Ban da wannan kuma, a cikin watannin Afrilu zuwa Yuni, GDPn ƙasar ya kai Yuan biliyan 29246.4, wanda ya ƙaru da kashi 0.4% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, sha’anin gona da na masana’antu sun samu karuwar Yuan biliyan 1818.3 da Yuan biliyan 12245, wanda ya ƙaru da kashi 4.4% da kashi 0.9% bisa na makamancin lokaci na bara, inda a sha’anin ba da hidimma ya samu ƙaruwar Yuan biliyan 15183.1, wanda ya ragu da kashi 0.4%.

Fassarwar Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *