Gida goma zamani goma: Wa zai sauya sheƙa gobe?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tun dawowa dimokuraɗiyyar Nijeriya a 1999 ‘yan siyasa da masana lamuran siyasa ko a ce masu sharhi a kafafen yaɗa labarai ke cewa mafi munin mulkin farar hula ya fi mafi kyawun mulkin soja inganci. Masu wannan batu na faɗar haka ne bisa yadda gwamnatin farar hula kan samu mulki ta hanyar zaɓe ko da kuwa zaɓen ta hanyar maguɗi ne, inda a gefe guda mulkin soja kan zama ta hanyar ɗaukar bindiga a ture gwamnatin farar hula kamar yadda ya faru a 1983 a ka kawar da gwamnatin marigayi Shehu Shagari ko kuma yadda soja ya ture soja a 1985.

Wani bambancin kuma shi ne yadda gwamnatin dimokuraɗiyya kan yi amfani da kundin tsarin mulki da majalisar dokoki da ke tsara doka inda shi kuma mulkin soja ke watsi da tsarin mulki ya ɗauki dokar majalisar ƙoli ta mulkin soja, inda wasu mutane ƙalilan masu gashin baki za su zauna su tsara abun da suka ga dama kuma ya zama doka ga ‘yan ƙasa ko su na so ko ba sa so.

A gaskiya a zamanin yau da a ke goyon bayan mulkin farar hula ko cin gajiyar sa, an rage cewa mafi munin sa ya fi na soja sakamakon yadda ‘yan siyasa kan zama gaggan ‘yan jari hujja, ramin kura sai ‘ya’yanta ta hanyar kuɗancewa a dare ɗaya da mayar da sauran jama’a ‘yan rakiya ko kuma ‘yan Allah-ya-ba-ku-mu-samu!.

Abun da ya ɗauki hankali na shi ne yadda kusan akasarin ‘yan siyasar Nijeriya ke marmarin tafiya da gwamnati da ke mulki ta salon arcewa daga adawa duk kuwa da yadda ta adawar wasu su ka tsinci dami a kala ko kuma ta nan ne su ka cimma burin ɗarewa kan karagar mulki da fitowa daga karkara zuwa birni.

Masana tsarin mulki na cewa duk ɗan siyasa na da ‘yancin shiga duk jam’iyyar da ya ke so ko ma iya gwada tsayawa takara ƙarƙashin inuwar jam’iyyar gashin kai wato mutum ya tsaya a matsayin ɗan takara ba tare da jam’iyya ba. Hakan dai bai fara yiwuwa ba a Nijeriya. Zuwa yanzu jam’iyyu biyu ne suka taɓa hawa kujerar shugabancin Nijeriya daga 1999 zuwa yau wato PDP da kuma yanzu APC duk da cewa APC ta kafu ne ta hanyar haɗakar wasu jam’iyyu da suka narke don takara mai ƙarfi a 2015.

Kamar yadda ya faru gabanin babban zaɓe a 2015 wasu gwamnoni na jihohi masu yawan ƙuri’a suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC duk da lokacin APC na matsayin ‘yar adawa, yanzu kuma wasu gwamnonin adawa ke shigowa APC mai mulki a na shekara ɗaya kafin shiga kakar kamfen ɗin 2023. Irin dalilan da gwamnonin kan bayar wajen sauya sheƙar ba ya zama wani dalilin matsin lamba don PDP ba ta kan kujera a halin yanzu ba kamar lokacin da wasu gwamnonin PDP suka yi fushi da tsohon shugaban jam’iyyar Alhaji Bamanga Tukur su ka yi ƙaura zuwa APC ba. Masana na cewa lissafin siyasa ne kawai don samun madafa a zaɓen mai zuwa tun da shi ɗan siyasar Nijeriya na son maƙalewa kan kujera ya zama daga gidan gwamnati sai in rai ya yi halin sa.

Duk da haka wasu misalai a baya na nuna ba lalle ne wanda ya sauya sheƙa ya iya zarcewa kan mulki ba in an duba misalin tsohon gwamnan Zamfara Mahmud Aliyu Shinkafi wanda ya sauya sheƙa daga ANPP zuwa PDP amma bai samu nasara a zaɓen 2011 inda tsohon gwamna Abdul’aziz Yari ya lashe zaven. Duk da haka wasu kuma da matsin lamba ya sa su sauya sheƙa ba don lissafin siyasa ba irin gwamnan Edo Godwin Obaseki da ya fice daga APC ya koma PDP ya lashe zaɓe karo na biyu. Tsohon mai gidan sa Adams Oshiomhole ya kasa karya shi duk da tsayin dakar da ya yi ba kamar yadda tsohon gwamnan Zamfara Ahmed Sani Yariman Bakura ya mara baya a ka kada Mahmud Shinkafi wanda gabanin nan mataimakin sa ne.

Babbar kotun tarayya a Abuja za ta fara sauraron ƙarar ƙalubalantar gwamnan Zamfara Bello Matawalle don sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Alƙalin kotun Jostis Inyang Ekwo ya karvi qarar daga lauyan masu ƙara Kanu Agabi, inda ya umurci a miƙa takardar gayyatar shari’ar ga gwamna Matawalle ta hanyar babbar hedikwatar APC. Wannan ya nuna cewa ba sai an yi ɗawainiyar shiga gidan gwamnati a Gusau don miƙa takardar ba.

Wasu ‘yan PDP daga Zamfara su biyu suka shigar da ƙarar bisa nuna dalilan cewa Matawalle ba shi da hurumin sauya sheƙa bisa hukuncin kotun ƙoli da ya ba shi dama ya zama gwamna bayan ture nasarar APC da gwamna mai jiran gado Shehu Mukhtar Kogunan Gusau.

Babbar jam’iyyar adawa PDP ta buƙaci a shigar da ita cikin masu shigar da ƙarar.

Mataimakin gwamnan Mahdi Aliyu Gusau bai bi gwamnan wajen sauya sheka ba.

“Shin abu ne mai yiwuwa a ce jam’iyyar da kotu ta ce ba ta da hurumin takara sannan kuma a ce za a koma cikin ta kuma ya zama ba a taka doka ba?” inji kakakin PDP Kola Ologbondiyan a zantawa da gidan talabijin na Channels kan sauya sheƙar da yin fatar kotu za ta umurci Matawalle ya yi murabus, bayan nan hukumar zave ta shirya sabon zave a wata uku.

Ologbondiyan ya ce tun da kotu ta yi hukunci cewa APC ba ta da hurumin tsayar da ‘yan takara a zaɓen na 2019, ai ba daidai ba ne a koma cikin ta kuma mataimakin gwamnan ma ya ƙi amincewa da ba da damar PDP ga APC.

In za a tuna tsohon gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari a gefe guda da Sanata Kabiru Marafa da ya ƙalubalanci yadda APC ta yi zaɓen fidda gwani; ba su amince da yadda a ka rushe shugabannin APC a Zamfara don shigowar Matawalle ba. Duk da haka ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi takarar Aminu Jaji ya ce haquri da mara baya ga ribar da APC ta samu ya fi alheri.

Yayin da PDP ke cewa ba wani dalilin rikici a cikin ta da zai sa wani sauyin sheƙa, APC na cewa ai wasu gwamnonin ma na kan hanya.

Za a fara sauraron qarar ce a yau Juma’ar nan 16 ga watan nan na Yuli da kuma a ke ganin qarar zai iya kaiwa har kotun ƙoli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *