Gidan Arewa da siyasar 2023

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gidan arewa wato ‘AREWA HOUSE’ da ke titin Rabah a anguwar Sarki a Kaduna garin gwamna nan ne gidan gwamnatin Arewa inda marigayi firimiya Sir Ahmadu Bello Sardauna ya zauna kuma har ma a nan ɗin ne masu kisan gilla ƙarƙashin Manjo Nzeogwu Kaduna su ka yi ma sa gillar.

Alamun gidan inda nan ne Sardauna ya ke kuma a nan a ke da cibiyar kayan tarihi ciki da wasu kayayyaki da marigayin ya yi amfani da su na nuna alfaharin Arewa da ma kai tsaye a ce kishin arewa mai jihohi 19. Haƙiƙa gidan na dukkan ’yan Arewa ne kuma ba a nuna bambancin addini, ƙabila ko siyasa.

Daraktan gidan na tarihi Dr.Shu’aibu Shehu Aliyu ya nanata cewa gidan na tuna baya ne don cigaba da jagorantar yankin arewa kan muradun son juna, zaman lafiya, raya kyawawan ɗabi’u da sauran su.

A fili ya ke cewa gidan Arewa ya zama waje ne da ƙungiyoyi daban-daban kan shigo su gudanar da taruka. Mutane kuma masu son duba bayanan tarihi kan kawo ziyara a zaga da su, su ganewa idanunsu yadda tarihin Arewa ya ke gabanin juyin mulkin 15 ga Janairun 1966.

Don haka har dai ka ga wani abu ya shafi gidan arewa to masu taro ne su ka zo gidan. Hakanan in ka ga jami’in gidan ya zo wani taro to an gayyace shi ne don tattaunawa lamuran da su ka shafi yankin Arewa. A ’yan kwanakin nan an fara wani taro na wani zauren arewa da kan gayyaci ’yan takarar neman shugabancin Nijeriya a 2023 don su zo su baje kolin su a mu su tambayoyi kan manufofinsu da irin alƙawarin abun da za su yi wa Arewa in Allah ya ba su nasara.

Irin wannan taron dai ba sabam ba ne kuma wani abu ma shi ne tsarin zauren ba ’yan takara daga arewa kaɗai ba ne ya shafi dukkan ’yan takarar daga kudu da Arewa. Tuni wasu daga ’yan takararsu ka halarci zauren. Bincike ya nuna zauren na da muradin gayyatar hatta ’yan takarar gwamna da majalisar dokokin taraiya don fahimtar muradunsu don jama’a su yi alƙalanci.

Haƙiƙa duk dan takara zai so a ce ya zo zauren ya kuma amsa tambayoyi yadda ya kamata don kyautata fatar hakan zai zama silar wasu ’yan Arewa su mara ma sa baya. Yankin Arewa na da girma da yawan masu kaɗa ƙuri’a don haka duk ɗan takara mai son yin tasiri to ya zama mai muhimmanci a gare shi ya bi duk hanyoyin da su ka dace wajen jawo hankalin masu kada ƙuri’a a yankin su mara ma sa baya.

A zaɓen 2015, haƙiƙa goyon bayan wasu gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP a yanzu daga Arewa ya taimaka ainun wajen lashe zaɓen shugaba Buhari. Gwamnonin da su ka sauya sheƙa daga PDP su ka dawo APC sun ƙara wa tafiyar shugaba Buhari ƙarfi. Gwamnonin sun haɗa da Rabiu Musa Kwankwaso na Kano, Aliyu Magatakarda Wamakko na Sokoto da Abdulfatah Ahmad na jihar Kwara.

A kudu an samu mara bayan gwamna Rotimi Amaechi na Ribas ne a lokacin da shi ma ya baro PDP ya shigo APC sai kuma Rochas Okorocha na jihar Imo da ya sauya sheƙa daga APGA ya dawo APC. A yayin da alamu ke nuna jan aiki ne a gaban mai neman shawo kan Arewa don samun goyon baya a zaɓen mai zuwa, ’yan siyasa za su so su bi hanyoyin shawo kan gwamnoni, masu faɗa a ji da ma miliyoyin masu kaɗa ƙuri’a na yankin.

Har yanzu in a ka lura ba faiyatacciyar alƙibla ta inda masu zaɓen na Arewa ke son zuba ƙuri’unsu. Ko ban ce komai ba duk mai bin tarihin babban zaɓen Nijeriya daga 2003, 2007, 2011 da 2015 ya san inda akasarin mutane su ka dosa amma yau fa? In ka zaga jihohi ba za ka ga karsashin mutane na son fitowa zaɓen ma ballantana a ce gadan takarar da za a samu rinjayen mutane sun mara ma sa baya.

Hakan ya na nuna wa imma ’yan yankin ba su kwashe niqa da waƙa ba a zaɓukan da su ka yi a baya ko kuma yanzu muradunsu na siyasa sun sauya. Akalla an ga rahoton wani gwamna a Arewa na cewa ɗaya daga manyan ’yan takara daga kudu ya na bin arewa bashi, ma’ana ya na bin Arewa bashin taimakawa da ya yi kenan a baya har ɗan Arewa ya samu shugabanci.

Na tabbata akwai waɗanda ba za su taɓa amincewa da cewa wani ɗan siyasa na bin yankinsu wani bashi ba. Abun ma la’akari ai a na maganar jam’iyyu ne kuma kowace jam’iyya na da ɗan takarar ta. Batun wannan gwamna zai fi kyau ya zama cewa akwai ɗan takarar da ke bin wasu ’yan arewa bashi shikenan.

Wato ma’ana duk yadda ka ke ganin alherin wani abu ko ribarsa to wani ba haka ya ke gani ba kuma shi ma ya na da gwaninsa daban da na ka. Ya na da muhimmanci ’yan siyasa su riqa tauna kalaman da su kan furta don kar hakan ya take haƙƙin wasu. Ba mamaki gidan arewa ya amince a gudanar da wannan taro inda shi kan sa gidan na da ruwa da tsaki a wannan zauren da kan gayyaci ɗan kowace jam’iyya kuma daga kowane yanki ya zo ya yi bayanansa don ba mamaki a rairaye shinkafa don fidda tsakuwa.

Idan irin wannan taro zai yi tasiri to ya na da kyau a rubuta dukkan abubuwan da a ka cimma kuma duk wanda ya halarci zaman ya rubuta yarejejeniya ko alƙawuran sa ya rantaba hannu a samu waje a adana don zama hujja. Arewa a yau na da buƙatu da yawa kusan fiye da kowane lokaci a baya.

Ga dai ƙalubalen tsaro, ga na talauci, ga wasu matasa fa yara da daman a gararamba kan tituna, ga wasu da lalaci ko jahilci, ga bambancin ƙabilanci da ma addini bisa tsarin rashin adalci. Iyayen arewa sun tafi sun bar yankin a matsayin ƙasa ɗaya al’umma ɗaya amma yau duk waɗannan turaku sun faɗi ƙasa warwas.

Gabanin zauren na gidan Arewa an samu ’Yan Bokon Arewa da su ka haɗa da malaman jami’a, ’yan siyasa da jagororin addini sun ƙaddamar da wata ƙungiyar da su ka yi wa taken ‘AREWA NEW AGENDA’ wato sabuwar ajandar Arewa.

Taron na da zummar fidda jerin buƙatun yankin arewa don miƙa wa duk ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa. Masana sun gabatar da jawabai kan tattalin arzikin yankin arewa da ya ƙunshi noma, kiwo, ma’adinai da yawan jama’a da matuƙar a ka yi amfani da su yadda ya dace yankin zai farfaɗo daga koma baya.

Shugaban sabuwar ƙungiyar Sanata Ahmed Muhammad Mo Allah-yidi ya ce, su na son faɗaɗa muradun Arewa ne fiye da yadda ƙungiyoyin yankin irin ƙungiyar tuntuɓar juna ta arewa da zauren dattawa su ke yi a halin yanzu. Mo’ Allah-yidi ya ce za su rubuta jerin buƙatun Arewa su miƙa su ga duk manyan ’yan takara da kuma zuba ido kan yadda za a yi da buƙatun bayan lashe zaɓe.

Da ya ke magana Bishop Jonathan Ma’aji ya ce lalle Arewa na da jan aikin dawo da yankin zamanin da ba a nuna bambanci a jamhuriya ta farko da a ka kifar a 1966. Shi ma shugaban sulhu tsakanin addinai a Jihar Kaduna Barista Tahir Umar Tahir ya nuna kwarin guiwar tafiyar za ta yi tasirin da a ke buƙata ta farfado da yankin arewa daga rarrabuwar kawuna da rashin tsaro.

Duk gwamnonin da a ka gaiyata na arewa ba su halarci taron ba amma hakan bai rage armashin sa ba tun da daraktan gidan tarihin Arewa ‘AREWA HOUSE’ Shu’aibu Shehu Aliyu ya halarta da tawagarsa. Duk da manufofin wannan taro amma ya samu caccaka daga gefe cewa ɗan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ne ya ɗauki nauyinsa don jan hankalin ’yan Arewa su kaɗa ma sa ƙuri’a ta hanyar hikimomi. Wannan dai raɗe-raɗi ne duk da an ga ’yan APC da dama sun halarci taron.

Ofishin ɗan takarar jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ɗan takarar na su ya ki zuwa zauren baje kolin manufofin ’yan takara a gidan AREWA a Kaduna don zargin taron na da manufar marawa wani ɗan takara baya.

Zauren na gidan Arewa da ke da gamayyar ƙungiyoyi na zama da dukkan ’yan takarar shugabancin Nijeriya don fahimtar irin alƙawuran da za su yi ga Arewa in an mara mu su baya.

A doguwar takarda da NNPP ta Turawa zauren don bayyana dalilan rashin bayyana, ta ce ranar da a ka gayyaci Kwankwaso ta zo daidai da zuwan wani ɗan takara inda bincike daga bisani ya nuna ɗan takarar PDP ne Atiku Abubakar.

Jigon kamfen din NNPP Buba Galadima ya ce ba lalle sai Kwankwaso ya je zauren ne za a fahimci shi mai kishin arewa ne ko ya na da manufofi masu kyau don raya Arewa ba.

Nan take ɗaya daga masu shirya taron Hakeem Baba Ahmed ya nesanta zauren da nuna ɓangare ya na mai cewa zargin ba shi da tushe.

Daraktan gidan Arewa Dr.Shu’aibu Shehu Aliyu ya ce, kasancewar gidan na marigayi Sardaunan Sakkwato ne Sir Ahamdu Bello, duk mai manufar kwarai ga Arewa na da hurumin ya zo ya bayyana manufofinsa.

Kammalawa;

A zaɓen nan na 2023 mai zuwa, an samu ƙungiyoyi na Arewa masu nuna muradin gabatar da buƙatun Arewa ga ’yan takara don yanke hanzari ga ƙorafin cewa rashin yin yarejeniya ke sa yankin ke tashi wayam kuma ba ikon cewa cas in an ce as.