Gidan rediyon Vision ya ja kunnen masu shirin ɓata ma sa suna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Kamfanin yaɗa labarai na ‘Vision Media Service’, masu gidajen rediyon Vision FM ya ja kunnen masu shirin ɓata ma sa suna ta hanyar yaɗa jita-jitar ƙarya a kafafen sadarwa na zamani.

A cikin wata sanarwa da babban jami’in gudanarwar kamfanin, Malam Shuaibu Mungadi, ya sanya wa hannun kuma ya raba wa manema labarai, ya ce, “abubuwan da ke faruwa a kafafen sadarwa na zamani dangane da kamfaninmu mai daraja, ya sa hukumar kamfanin ta fitar da wannan sanarwa da nufin gyara kura-kuren da wasu tsirarun mutane da wasu abokan aikin kamfanin suka yi.”

Sanarwar ta ce, “duk da cewa ba al’adarmu ba ce mu shiga al’amarin mutane wajen bayyana ra’ayoyinsu game da kamfaninmu ko kuma a kanmu, amma ya zama dole mu fayyace yunƙurin da masu aikata ɓarna suke shirin yi a halin yanzu na ɓatar da jama’a.”

“Don haka, kamfaninmu, kamar sauran kamfanoni da yawa, bai fi ƙarfin samun yin kuskure ba, musamman dangane da fannin aiki, ƙirƙira da dai sauransu. A irin wannan yanayi, kamfaninmu yana bin matakan cikin gida daidai da ƙa’idojin aiki, Dokokin Ma’aikata na Nijeriya da sauransu, kuma ba tare da bin ra’ayin jama’a ko tsangwama ba.”

Sanarwar ta ce, “don haka a duk lokacin da muka yi wani da ba a gamsu ba, ma’aikatan da abin ya shafa za su iya ɗaukaka ƙara a ciki ko kuma neman gyara a wuraren da suka dace. Don haka abin takaici ne yadda wasu daga cikin ma’aikatanmu da aka kore su daga kamfanin, saboda rashin ɗa’a, rashin gudanar da aiki yadda ya kamata, zamba da rashin aikin yi, suka zaɓi rashin nuna nadama.”

Ya ce, “ga abokin hulɗarmu, Mahadi Shehu, wanda ya yanke shawarar yin yadda ya ga dama, har ya kai ga kai farmaki ofishinmu na Kaduna kuma ya kausasa murya tare da ƙaddamar da kamfen na zagon ƙasa ga mai girma shugabanmu, ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta na zamani, mu na ɗaukar matakan da suka dace na doka da neman gyara ba daga gare shi kaɗai ba, har ma da masu yaɗa da’awarsa na vatanci a socal midiya da sauransu.

“Lallai mu na godiya ga masu ruwa da tsaki, abokai da masu fatan alheri bakiɗaya. Al’ada ce a cikin tafiyar rayuwa, don neman taimako ko karɓar taimako daga mutane. Haka zalika, mu na farin cikin cewa, Mahadi Shehu bai tuhume ko zarge mu da wasu munanan manufofi ba, ko kuma yin wani abu ba bisa ƙa’ida ba wajen samun irin wannan tagomashi da aka yi mana. Ba mu ne na farko ba kuma tabbas ba za mu kasance na ƙarshe da za mu fuskanci irin waɗannan abubuwan ba. Godiyarmu ba ta da iyaka ga duk waɗanda suka taimaka mana ta kowacce hanya.”