Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Kwamitin Aikin Mayar da Alkhairi da Alkhairi ƙarƙashin ƙungiyar Giɓing Back Initiatiɓe ta tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa, wanda Sadaukin Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki ke jagoranta, tare da wasu mambobi 7, sun samu nasarar kammala, aikin rabon tallafin kayan abinci a ɗaukacin ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato 23, cikin nasara.
Kwamitin ya gudanar ayyukan alkhairin da aka tsara rabawa al’ummar Jihar Sakkwato ne ga mabuƙata, ‘yan gudun hijira, masu lalura ta musamman, marayu, uwayen marayu, masu rashin lafiyar taɓin hankali, tsofaffi, limamai da sauran ɓangarorin jama’a. A tsarin rabon da aka yi, kwamitin ya soma ne da rabon abinci ga ‘yan gudun hijira da ke ƙananan hukumomi uku, inda aka raba musu kimanin buhunan abinci guda 900 da kuɗi Naira Miliyan 9, yayin da ƙananan hukumomi 20 aka bai wa kowaccen su buhuna 100 da kuɗi Naira Miliyan 1 da rabi.
Shugaban Kwamitin Malam Muhammad Lawal Maidoki ya yi kira ga waɗanda suka amfana da kada su ci su kaɗai su ma su tallafawa mabuƙata na tare da su, tare da kiran su riƙa yi wa wanda ya ba da tallafin addu’a, Allah Ya biya shi. Sannan ya kuma yi kira ga al’umma masu hali su riƙa fitar da Zakka da ba da Waƙafi kamar irin wannan da Garkuwar Sakkwato ya yi.
Sadaukin Sakkwato ya yi godiya ga Gwamnatin Jiha da Majalisar Sarkin Musulmi da uwayen ƙasa da ƙananan hukumomi kan goyon bayan da suka bayar da ya taimaka ga samun nasarar shirin.
Shi ma a nasa ɓangaren, Sakataren Kwamitin Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa, ya bayyanawa manema labarai cewa, shirin ba shi da alaƙa da siyasa ko ɓangaranci, an yi ne domin kawo ɗauki ga halin matsin rayuwa da al’umma suke ciki, maimakon barin Gwamnati ita kaɗai da ɗawainiyar kula da jama’a.
Wasu shugabannin ƙananan hukumomi da uwayen ƙasa da shugabannin ƙananan kwamitoci sun yaba wa tsohon Gwamnan kan wannan aikin, tare da kira ga sauran ‘yan siyasa da masu sukuni da su yi irin wannan aikin, don ƙara tallafawa al’ummarsu.
Sarkin Malaman Sakkwato, Sheikh Umar na Malam Boyi, ya yi nasihohi akan muhimmancin fitar da Zakka da ba da sadaka, da neman Ilimi Don taimakawa alumma. Malam Kabiru Shehu Binji, Alhaji Nasiru Bafarawa, Alhaji Ahmad Gyarafshi, Prof. Malami Umar Tambuwal, sun yi ƙarin haske akan ɗimbin ayyukan da za a aiwatar nan gaba.
Wasu bayin Allah da suka amfana sun yi godiya da addu’a ga tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa da ‘yan kwamiti da duk masu hannu cikin wannan aikin alkhairin.